Daga Ammar M. Rajab Gwamnatin jihar Kaduna ta gudanar da wani babban biki yau domin murnar cikar gwamnan jihar, Sanata (Dr.) Uba...
Daga Ammar M. Rajab
Gwamnatin jihar Kaduna ta gudanar da wani babban biki yau domin murnar cikar gwamnan jihar, Sanata (Dr.) Uba Sani shekaru biyu a matsayin Gwamnan jihar Kaduna, inda ya ƙaddamar da wata babbar hanya a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari — wata alama dake nuni da ci gaban da gwamnatinsa ke samu a fannin gine-ginen ababen more rayuwa.
Taken taron shi ne: “Shekara 2 ta Mulkin Mai Girma, Sanata (Dr.) Uba Sani,” wanda manyan jami’an gwamnati, shugabannin al’umma, jiga-jigan jam’iyya, da mazauna yankin suka halarta cikin farin ciki da nuna goyon baya.
Muhimman abubuwan da suka gudana a wajen taron sun haɗa da addu’ar buɗe taro, saƙonnin fatan alheri, da jawaban wasu manyan baƙi ciki har da Manajan Darakta na Hukumar Kula da Hanyoyi ta Kaduna (KADRA), Kwamishinan Ayyuka da Ababen More Rayuwa, da Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Sabon Gari.
Babban abin da ya fi ɗaukar hankali a bikin shi ne ƙaddamar da sabuwar hanya mai tsawon kilomita 8.8 daga Dogon Bauchi zuwa Unguwan Gwado, Hayin Fulani, Kakiyeyi har zuwa Dakace. Hanyar na ɗauke da gada mai tsawon mita 105 wacce ta haɗa Ƙananan Hukumomin Sabon Gari da Zariya — muhimmin aiki a fannin ci gaban yankin.
A cikin jawabin sa, Gwamna Uba Sani ya bayyana aikin a matsayin shaida ta yadda gwamnatinsa ke nuna ƙwazo wajen kawo ci gaba mai inganci ga kowa da kowa.
“Wannan hanya wata alama ce ta matakin da muke kai wajen inganta ababen more rayuwa a jihar Kaduna. Ƙaddamar da wannan hanya da gada mai tsawon mita 105 wata alƙawari ce da muka cika. Hakan ya kuma nuna yadda muke ƙoƙarin rage bambanci tsakanin karkara da birane,” inji shi.
Gwamnan ya jaddada cewa hanyoyi ba kawai gine-gine ba ne, amma su ne ginshikan ci gaba ta fuskar tattalin arziƙi, zamantakewa, haɗin kai, da tsaro mai ɗorewa.
“A gare mu, hanya ba kawai hanya ba ce. Hanya tana kawo ci gaba. Kowacce taku na kawo haɗin kai, yana ƙara bunƙasa kasuwanci, yana inganta haɓaka kasuwanci, asibitoci da kuma ilimi,” ya jaddada.
Gwamna Sani ya ƙara da cewa wannan hanya za ta inganta harkokin tsaro da tattalin arziƙi a tsakanin mutanen Sabon Gari da Zariya. Ya kuma buƙaci al’umma da su kula da wannan katafaren aiki, tare da nuna godiya bisa goyon bayansu.
“Ina alfahari da mutanen Sabon Gari. Goyon bayanku da jajircewarku abin yabo ne. Wannan aiki naku ne,” ya bayyana.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, Honarabul Jamilu Abubakar Albani, ya yabawa Gwamnan bisa jajircewarsa wajen kawo ayyukan ci gaba tun a matakin farko
“Mai Girma Gwamna, wannan hanya ɗaya ce daga cikin shaidar jajircewarka wajen inganta rayuwar talakawa. Sabon Gari na matuƙar godiya,” inji shi.
Ya sake jaddada biyayyarsa tare da alƙawarin ci gaba da nuna cikakken goyon baya ga Gwamna da duk wani burikansa a gaba.
“A gaban Mai Girma Gwamna, ina tabbatar da cewa dukkan jiga-jigan jam’iyyar APC a Sabon Gari na tare da kai da manufofinka na ci gaban al’umma. Muna nuna cikakken goyon baya ga tazarcen ka,” ya tabbatar.
Wasu mazauna yankin suma sun bayyana farin cikinsu. Muhammad Sani daga Kakiyeyi ya shaida wa wakilinmu: “Wannan hanya ta sauya rayuwarmu gaba ɗaya. Muna shan wahala, musamman a damina. Gwamna Uba Sani ya tuna damu sosai.”
Wata mazauniyar yankin, Aspina Daniel, ta yi magana kan muhimmancin gadar: “Gada mai mita 105 tamkar falala ce gare mu. A da sai mun ɗauki awanni kafin mu ƙetare idan ruwa ya yi. Yanzu muna jin daɗin wannan aiki mai ƙima.”
Bikin ya ƙare da ɗaukar hoto tare da ficewar manyan baƙi, yayin da jama’a suka bar wajen cike da ƙwarin gwiwa da fatan ci gaba da shimfiɗa ayyukan ci gaba.
No comments