Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CAGRAT Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Kan Shugabancin Hukumar NCDC

Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar hadin kai da cigaban yanki (Community Association for Grassroot Transformation) ta nuna rashin jin dadint...



Daga Awwal Umar Kontagora

Kungiyar hadin kai da cigaban yanki (Community Association for Grassroot Transformation) ta nuna rashin jin dadinta kan shugabancin sabuwar hukumar cigaban yankin arewa ta tsakiya na gwamnatin tarayya.

Tunda farko a wani taron manema labarai da kungiyar ta kira bisa jagorancin shugabanta na kasa, Alhaji Muhammadu Dagaci Etsu-gaie, kungiyar ta bayyana cewa a nadin shugabancin hukumar da gwamnatin tarayya ta yi ba a yiwa jahohin Neja, Kwara da Kogi adalci ba.

A takardar manema labarai da kungiyar ta fitar, ta bayyana cewar idan an duba mukamin shugaban hukumar da babban manajan hukumar an bada su ne a jahohin Fulato da Benue yayin da aka kafa sakatariyar hukumar a jihar Nasarawa, wanda wannan ba daidai ba ne domin dukkaninsu sun fito a yanki daya.

Wani abin takaici da gwamnatin tarayya tayi mukaman mambobin hukumar ba a yi nazari wajen zakulo su ba, domin idan ka dauki jihar Neja a misali, akwai kabilu da dama kuma mabiya mabanbantan addinai, amma kabilar Nupe da ke da kashi saba'in ba su samu mukamin komai a hukumar ba.

Muna jawo hankalin gwamnatin tarayya da ta sani cewar lokacin siyasa ne kuma duk wani cigaba a tafiyar siyasa akan yi raba daidai ne duba da irin gudunmawar da kowani yanki ta bayar.

Idan ana son hadin kai da cigaban kasa, ya kamata a daina danniya da nuna fifiko wajen rabon mukaman siyasa, amma idan ka dubi yankin arewa ta tsakiya gwamnatin tarayya ta mayar da ita baya, duk wani abinda ya shafi yankin nan ana kokarin danne shi, yanzu mukamin shugabancin jam'iyyar APC a matakin kasa da yake hakkin mu kiri-kiri ya zama wasan yara, ga aikin madatsar ruwan Baro da muke kyautata zaton idan an kamnala shi zai samar da gurabun ayyuka ga dubban yan kasar nan, an watsar da shi.

Sannan akwai ayyukan hanyoyin gwamnatin tarayya na sama da biliyan dari bakwai da za a yi a jahohi goma sha uku amma jihar Neja da tafi kowace jiha a kasar nan yawan hanyoyin gwamnatin tarayya an ware jihar ba ta cikin wannan gajiyar.

Muna kira ga gwamnatin tarayya da yan majalisun dokoki na tarayya da su gaggauta farkawa da illar da ake son yi mana, muna kara tuni ga shugabanni da su tuna lokacin siyasa ne, kuma kuri'ar mu yana da tasiri a zabukan kasar nan, kuma dukkan zagon kasar da ake mana muna kallo. Yan majalisun mu na tarayya da su sani ba fa kawunansu suke wakilta ba, jama'a ne suka zabe su bisa amana da ganin zasu tsaya tsayin daka wajen ganin al'ummomin su na cin gajiyar ayyukan gwamnatin tarayya.

Babawachiko Yahaya, mataimakin shugaban kungiyar ta kasa, yace muna jawo hankalin majalisar tarayya da su gaggauta nazartar abinda ke faruwa domin gaggauta yin gyara ga wannan kuskuren da ake son yi, domin ba zamu zura idanu ana cigaba da take hakkin mu na arewa ta tsakiya ba.

Mun fahimci wadanda ya kamata su rika magantawa ba sa iya magana, shi yasa muka fito muka fara magantawa da kan mu, wanda kuma mun kuduri aniyar cigaba da wayar da kan al'ummomin da abin ya shafa dan ganin ba a bar mu a baya wajen cin gajiyar romon dimokuradiyya.

Comr. Sani Musa Sahorami, shi ne mataimakin shugaban matasa na kasa na kungiyar, yace mata da matasa suna takaicin abubuwan da ke faruwa duk da irin jajircewarsu wajen baiwa gwamnati goyon baya akan kudurorinta amma duk wani aikin cigaba na gwamnatin tarayya mu ake bari a baya.

CAGRAT dai ta bukaci gwamnati ta gaggauta gyara mukaman hukumar tsakanin wadannan jahohin da abin ya shafa. Kuma a tabbatar an yi adalci ga jahohin nan shida akan wadannan mukaman.

Kungiyar dai tace ya kamata a rika nazari wajen lura da yawan kabilu da addinai wajen bada mukaman siyasa.

Muna kira ga yan majalisar tarayya musamman wadanda suka fito daga yankin arewa ta tsakiya, musamman ma yan jihar Neja su zama masu kishi da kokari wajen kawo cigaba a yankunansu, matsayi ko mukamin siyasa ba yana nufin kawo rarrabuwan kawuna ba ne tsakanin al'ummominsu ba, haka zai iya shafar makomarsu da cigaban da suke muradi.

Duba da tarihi kan abubuwan da ke faruwa a kasar nan, an dade ana yiwa yankin arewa ta tsakiya cin kashin kaji tun zuwa wannan jam'iyyar ta APC a madafun ikon kasar nan, muna kira da a gaggauta yin gyara kar wankin hula ya kai mu dare. 

No comments