Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙaramar Hukumar Sabon Gari Ta Ƙaddamar da Manyan Ayyukan Gina Tituna

Daga Nidala Muhammad Rabiu A wani muhimmin mataki na gudanar da aiki mai ɗorewa da kuma bunƙasa tattalin arziƙi, Shugaban Ƙarama...

Daga Nidala Muhammad Rabiu

A wani muhimmin mataki na gudanar da aiki mai ɗorewa da kuma bunƙasa tattalin arziƙi, Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, Hon. Jamilu Abubakar Albani, a ranar Talata, 13 ga Mayu, 2025, ya ƙaddamar da manyan ayyuka guda uku na gina tituna da nufin sauya fasalin yankin da kuma inganta rayuwar mazauna yankin.

A yayin da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamarwar, shugaban ya bayyana wannan rana a matsayin “muhimmin rana” a cikin ƙoƙarin sake fasalin ƙaramar hukumar ta hanyar shirye-shiryen gina ababen more rayuwa daban-daban. Ya ce, waɗannan ayyuka wani ɓangare ne na hangen nesa domin gina tubalin ci gaba mai ɗorewa da samar kyakkyawan makoma.

Aikin farko shi ne gina titin gadar sama (flyover) a Kwangila a gundumar Hanwa, wanda ake sa ran zai zama muhimmin hanyar haɗa sufuri tsakanin Arewa da Babban Birnin Tarayya, Abuja. Ana kuma sa ran cewa titin gadar zai ƙarfafa harkokin kasuwanci da haɗin kai tsakanin al’umma a yankin.

Na biyu kuwa shi ne gina gada a Palladan cikin gundumar Basawa, wanda aka tsara domin rage cunkoso da sauƙaƙa zirga-zirga a yankin. Ana sa ran wannan gada za ta ƙara faɗaɗa harkokin kasuwanci da sauƙaƙa zirga-zirga a tsakanin mazauna yankin.

Aiki na uku shi ne gina titin Sakadadi a cikin gundumar Dogarawa. Wannan aikin na da nufin inganta zirga-zirga da samar da sauƙin gudanar da ayyuka da sauran muhimman abubuwan more rayuwa, wanda hakan zai ƙara taimakawa wajen sufuri a yankin. 

“Waɗannan ayyuka sun nuna jajircewarmu wajen inganta rayuwa da ci gaban al’ummarmu,” in ji Shugaban. “Za a aiwatar da su cikin gaskiya, riƙon amana da bin ƙa’idojin inganci na aiki.”

Sai dai ya roƙi mazauna yankin da su ba da haɗin kai ga ‘yan kwangila da hukumomin gwamnati domin ganin an kammala ayyukan cikin lokaci da nasara.

Ya ƙara da cewa, “Mu haɗa hannu domin gina Sabon Gari mafi soyuw inda ‘yan ƙasa za su zauna cikin kwanciyar hankali, su gudanar da ayyukan su na yau da kullum, kuma su cimma burinsu cikin ‘yanci da aminci.”

Shugaban ya kammala jawabinsa da addu’o’i da fatan alheri ga ƙaramar hukumar, Jihar Kaduna da ƙasa baki ɗaya.

Taron ya samu halartar manyan baki, shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki, waɗanda suka nuna farin ciki da fatan alheri kan yadda ayyukan za su shafi tattalin arzikin yankin da zamantakewar al’umma.

Daga cikin waɗanda suka halarta akwai Kwamishinan Gidaje da Raya Birane na Jihar Kaduna, Aminu Abdullahi Shagali; ɗan majalisar dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazaɓar Sabon Gari, Nasiru Idi; Mataimaki na Musamman ga Gwamnatin Jihar Kaduna kan Harkokin Ma’aikata; shugabannin jam’iyyar APC a matakin ƙaramar hukuma; da sauran manyan mutane.

No comments