Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tsaro: Jami'an Tsaron Ƙasar Nan Sun Yi Ƙaranci Wajen Tunkarar Wannan Matsalar - Wana

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar baiwa jami'an tsaro umurni harbe duk wanda suka gani da makami ba zai wadar ba wa...

Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar baiwa jami'an tsaro umurni harbe duk wanda suka gani da makami ba zai wadar ba wajen magance matsalar tsaro a kasar nan. Mai fashin baki akan harkokin yau da kullun kuma jigo a jam'iyyar APC, Alhaji Awaisu Giwa Wana ne ya bayyana hakan lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Minna.

Alhaji Awaisu, ya cigaba da cewar muna da majalisar tarayya ta kasa kuma muna da na jahohi, koda sun zartas da kudurin doka akan hakan ba zai wadatar ba, dole sai an kara yawan jami'an tsaro, domin idan mun duba bangaren yan sanda kawai a kiyasi ba zasu wuce dubu dari uku ba. Kuma maimakon aikin tsare rayuka da dukiyoyin al'umma sun koma tsare shugabanni da manyan yan siyasa, domin yanzu kashi biyu cikin ukun yan sanda sun koma gadin shugabanni ne da manyan yan sanda, sauran da suka rage kuma ba su da gatan samun irin wannan damar ba su da isasshen kayan aikin da zasu rika anfani da shi.

Yau matsalar tsaro a kasar nan ba cikin birni ba sannan ba cikin daji ba. Yan bindiga sun mamaye daji suna cin karen su ba babbaka, yayin da a cikin birane kuma matasa da ake tsammanin su ne manyan gobe sun dauki makamai sun kai hari ga al'umma da sunan kwacen waya da wasu muhimman abubuwa.

Idan gwamna ya bada umurnin a harbe wanda aka gani da makami yana da hurumin hakan domin shi ne jagoran tsaro a jiharsa, amma wadanda aka baiwa damar yin aikin wani tanadi gwamnatin tayi masu, yau ko kama yaro aka yi da laifin ta'addanci ko an kai shi gaban kotu gobe za ka ga ya fito, shin su waye masu amso masu laifin.

Yana da kyau, majalisun dokoki su samar da tsauraran dokoki kuma a tabbatar an yi aiki akan su, sannan a tabbatar an kara yawan jami'an tsaro amma za ka wuri mafi hatsari da ke dauke da daruruwan jama'a yan sandan da za ka gani ba su fi uku zuwa biyar ba.

Amma da zaran gwamnati na son rusa wani ko wasu da take ganin barazana ne gare ta za ka an debo jami'an tsaron hadin guiwa kamar zasu yaki.

Matsalar tsaro a kasar nan ya zama wani abu daban domin rashin yarda da ya mamaye zukatan yan Nijeriya, dan kudu bai yatda da dan arewa ba, shi ma dan arewa bai yarda da dan kudu ba. Haka uba bai yarda da dansa ba, mace ba ta yarda da mijinta ba.

Dole idan ana son gyara da gaske ayi taron kasa, dan tattaunawa kan halin da ake cikin kamar yadda ya faru lokacin Janar Babangida da Marigayi Sani Abachi, idan an tattauna an samu mafita a zartas da shi da gaske ta yadda kowa zai yi amannar da gaske ne gwamnati ke yi.

Amma irin wannan umurnin da gwamnatocin jahohi ke zartaswa va abinda zai magance, domin ba a dauki turbar da ta dace ba. Kullun ina fadin cewar abinda ya hanawa kasar nan cigaba shi ne rashawa.

Gwamnati ta dakile shi da gaske kuma ayi hukunci mai tsanani, idan an ce wani ya aikata irin wannan laifin ba zai yarda ba. Amma kasar mu kasa ce da duk irin laifin da ka aikata muddin kana da daurin gidi da kudi ko an tafi kotu sai dai ayi ta wasan kwaikawayo.

Manazarcin yace ko a tsarin shugabancin kasar nan saboda tasirin rashawa muddin kana da kudi ko laifin ka za ka iya samun shugabanci ba tare da wahala ba, ta ina ne mai laifi zai iya magance ko daukar mataki akan wani mai laifin tunda shi ma tudun da ya hau ke nan.

Dole ne gwamnati ta yaki da rashawa da gaske, dole ne a samar da karin yawan jami'an tsaro kuma dole a tabbatar an samar masu kayan aiki ta yadda zasu samu saukin gudanar da ayyukan su. Duk wani a harbe ba maganin da zai yi face su jami'an tsaron su yi anfani da yan makaman su wajen kare kawunan su.

No comments