Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Zamfara Ta Haɗa Gwiwa Da Oracle A Landan Don Bunƙasa Fasahar Zamani

Gwamnatin Jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da Jami'ar Oracle domin saka hannun jari a harkar inganta rayu...

Gwamnatin Jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da Jami'ar Oracle domin saka hannun jari a harkar inganta rayuwar matasa, inganta ƙarfin ma’aikata, da kuma tattalin arziki na zamani a ƙarƙashin shirin Bunƙasa Fasaha na Jami’ar Oracle (SDI).

An sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Talata 29 ga Afrilu, 2025 a Ofisoshin Oracle da ke Landan a Ingila.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, wannan aiki zai samar da haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Bunƙasa Fasahar Zamani ta Zamfara (ZITDA) da Oracle.

Tawagar jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta haɗa da sakataren gwamnatin jihar, da masu ba da shawara na musamman guda biyu, da babban sakataren ZITDA, tare da Siobhan Wilson, shugaban Oracle na Ingila da kuma babban mataimakin shugaban EMEA.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai muhimmanci tare da Oracle don bunƙasa fasahar dijital a faɗin jihar, wanda aka samu ta hanyar Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), haɗin gwiwar za ta yi amfani da ƙwarewa da ayyukan koyo na makarantar Oracle da jami'ar Oracle a ƙoƙarinsu na kawo sauyi.

“Haɗin gwiwar yana nuna sadaukar da kai ga ilimi da saka hannun jari a makomar matasan Zamfara, ma’aikata, da tattalin arzikin dijital.

"Makarantar Oracle, shirin ilimi na taimakon jama'a na duniya yana koyar da ilimin fasaha, gami da manhaja da samun damar sanin ilimin fasahar software na kwamfuta ga malamai da ɗalibai a duk duniya.

“Tare da tallafin Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), za a samar da waɗannan albarkatun ga ingantattun manyan makarantu a faɗin Zamfara.”

“ZITDA za ta taimaka wajen jagorantar ayyukan makarantar Oracle Academy a cikin babbar manhajar karatu ta Zamfara, tana ba wa malamai kayan aiki da albarkatun da suke buƙata don koyar da ɗalibai dabarun fasaha da

No comments