Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

MATSALAR TSARO: Gwamnonin Inyamurai Sun Kafa Ta Su Rundunar Tsaron

Jaridar Dimokuradiyya ta labarto cewa; gwamnonin Inyamurai dake kudu maso gabashin kasarnan sun ayyana ƙaddamar da runduna ta mu...

Jaridar Dimokuradiyya ta labarto cewa; gwamnonin Inyamurai dake kudu maso gabashin kasarnan sun ayyana Æ™addamar da runduna ta musamman da za ta rika bai wa yankinsu su tsaro. Sunan rundunar tsaron da suka kafa ‘Ebube Agu’.

Bayanai sun nuna cewa; gwamnonin sun jaddada cewa har yanzu haramcin da aka sanya kan kiwo a yankin yana nan daram, inda suka umurci sabuwar hukumar tsaron ta tabbatar da an mutunta dokar da suka sanya.

Majiyarmu ta ruwaito cewa gwamnonin sun hadu ne a Owerri, babban birnin jihar Imo, inda suka tattauna da shugabannin hukumomin tsaron yankin.

MuÆ™addashin babban sufeton Æ´an sanda na Æ™asa Usman Baba ya tura wakilansa karkashin jagorancin mataimakin Sufetan ‘yan sanda.

A ranar Litinin da ta gabata, Æ´an bindiga suka farwa hedikwatar Æ´ansanda a Owerri, tare da kona motoci 38 da sakin fursunoni 1,844.

No comments