Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Litinin, ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen ganin ta farfado da bangaren ilimi a dukkannin mat...
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Litinin, ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen ganin ta farfado da bangaren ilimi a dukkannin matakai.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar bazata a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta lafiya da ke Tsafe.
Sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ya ce an kai ziyarar ne domin duba irin kalubalen da ke addabar makarantar.
Sanarwar ta kara da cewa: “Shugaban makarantar, Hamisu Yusuf Yelwa ya zagaya da Gwamna Lawal, inda ya duba tare da tantance yanayin ajujuwa da dakunan kwanan dalibai.
“Daga cikin gine-ginen da aka duba akwai ginin ajujuwa, rukunin Dauda Lawal Dare da Gwamnan ya gina a wani bangare na ayyukan taimakon da ya yi shekaru kafin a zabe shi.
“A lokacin da Gwamna Lawal ya ke tantance dakunan kwanan dalibai mata, ya tattauna da wasu daliban da suke kwana a ciki, inda suka bayyana masa manyan matsalolin da suka sa dakin kwanan dalibai ba shi da kyan zama.
“Gwamna Lawal ya damu matuka da irin yanayin da ya gani na lalacewar ababen more rayuwa a kwalejin, inda kuma ya sha alwashin daukar matakin gaggawa wajen magance matsalar.
“Ya umurci shugaban makarantar da ya bayar da cikakken rahoton bukatunsu, a kokarinsa na yin garambawul a fannin ilimi a jihar”.
No comments