Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jami’ar MAAUN ta sanyawa makarantar Karatun Lauya sunan Uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu

Hukumar kula da Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya ta sanya wa ginin makarantar koyon karatun lauya sunan matar shugaban ...



Hukumar kula da Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya ta sanya wa ginin makarantar koyon karatun lauya sunan matar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kuma uwargidan shugaban kasa, Misis Oluremi Tinubu.

Wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa ta jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ne ya bayyana hakan a wajen kaddamar da dakin taro na Maryam Abacha a hukumance da uwargidan shugaban kasar, Misis Oluremi Tinubu da kuma uwargidan mataimakin shugaban kasa Nana Shettima suka kaddamar a cibiyar ci gaban mata ta kasa dake Abuja a ranar Asabar, 5 ga Agusta, 2023.

Ya ce hukumar gudanarwar Jami’ar ta yanke shawarar sanya wa ginin sunan Uwargida Oluremi Tinubu ne saboda kokarinta na inganta zaman lafiya da hadin kai da kuma kasancewarta ‘yar Nijeriyar da ba ta da kabilanci.

“Mun ga ya dace mu karrama Misis Tinubu bisa tawali’unta da kyautatawarta, kuma fiye da hakan, saboda kokarinta na wanzar da zaman lafiya da hadin kai a kasar nan.

“Wannan wani aiki ne na musamman wanda aka yi shi da nufin bunkasa hadin kai tare da wanzar da zaman lafiya, kuma ya kamata dukkan shugabanni su yi koyi da shi ba tare da la'akari da jinsi a kasar ba”, in ji Farfesa Gwarzo.

Farfesa Gwarzo ya ce Hukumar ta kuma yanke shawarar sanya wa ginin sunan Uwargidan Shugaban kasar ne domin a fahimci irin girman kyakkyawan salon shugabancinta na rashin ji ji da kai da kuma saukin kai wanda ya kamata sauran shugabannin mata su yi koyi da ita.

Ya ce ana sa ran uwargidan shugaban kasar za ta kaddamar da ginin a ranar da za a bayyana a nan gaba.

A yayin da take mayar da jawabi, Misis Tinubu ta bayyana jin dadin ta ga Farfesa Gwarzo bisa zabo ta a matsayin wacce ta cancanta da wannan karramawar, inda ta yi addu’ar Allah madaukakin Sarki da ya ci gaba da ba shi karfin guiwa wajen bunkasa ilimi a kasar nan.

Uwargidan shugaban kasar ta labarta cewa ta yi hidimar kasa (NYSC) na shekara daya a Kano, ta kuma gode wa Farfesa Gwarzo bisa karramawar da ya yi mata.

 

No comments