Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaddamar da wasu matakai daban daban da za su zaburar da tattalin arzikin kasar da zummar s...
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaddamar da wasu matakai daban daban da za su zaburar da tattalin arzikin kasar da zummar shawo kan kuncin rayuwar da jama’ar kasar suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur.
Yayin da ya ke yi wa jama’ar kasar jawabi ta kafar talabijin, Tinubu ya ce cire tallafin man ya zama wajibi lura da yadda wasu ‘yan tsiraru kawai ke amfana da shi, yayin da akasarin jama’ar kasar ke shan wahala.
Shugaban ya ce a cikin watanni biyu da suka yi a karagar mulki, gwamnatin sa ta yi nasarar ceto sama da naira triliyan guda daga cikin makudan kudaden da ake zubawa a matsayin tallafin man, wadanda za’a karkatu su wajen bunkasa harkar ilimi da harkokin kula da lafiya da kuma samar da kayan more rayuwa.
Tinubu wanda ya ce ya fahimci halin kuncin da ‘yan Najeriya suke ciki, ya kuma bayyana shirye shirye da dama da gwamnatin sa za ta aiwatar wajen samar da rance ga masu kanana da matsakaitan masana’antu domin bunkasa harkokin su ta yadda za su amfana ta hanyar biyan kashi 9 na kudin ruwa.
Shugaban ya kuma jinjinawa masu kamfanoni da masana’antu saboda dagewar da su ke da ita wajen ci gaba da harkokin su a cikin irin wannan yanayi mai tsauri.
Shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin sa na tattaunawa da kungiyoyin kwadago da zummar kara albashin ma’aikata saboda tinkarar halin da ake ciki, yayin da kuma ya ce zai aiwatar da shirin sa da ya yi alkawari na tallafawa marasa karfi a cikin al’umma.
No comments