Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NFF Ta Nada Finidi George Kociyan Super Eagles

  Hukumar kwallon kafar Najeriya, NFF ta nada Finidi George a matakin sabon kociyan Super Eagles. George, ya yi wata 20 yana aikin mataimaki...

 


Hukumar kwallon kafar Najeriya, NFF ta nada Finidi George a matakin sabon kociyan Super Eagles.

George, ya yi wata 20 yana aikin mataimakin Jose Santos Peseiro, wanda ya ajiye aikin, bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Afirka da Super Eagles ta yi ta biyu a Ivory Coast a bana.

Haka kuma ya ja ragamar tawagar Najeriya a matakin kociyan rikon kwarya a wasan sada zumunta biyu da ta buga a Morocco a watan jiya.

Ya doke Ghana 2-1 a wasan farko, hakan ya kawo karshen rashin nasara a kan Black Stars daga Super Eagles cikin shekara 18, amma an doke shi 2-0 a karawa da Mali a wasan na sada zumunta.

George, wanda yana cikin Æ´an wasan da suka dauki kofin nahiyar Afirka a Super Eagles a1994 a Tunisia, ya buga mata wasa 62, ya wakilce ta a gasar kofin duniya a 1994 da 1998.

Haka kuma ya lashe lambar zinare da ta azurfa da ta tagulla a gasar kofin nahiyar Afirka a 1992 da 1994 da 2000 da kuma 2002.

Mai shekara 52 tsohon dan kwallon Ajax da Real Betis ya fara taka leda a Calabar Rovers da Sharks FC daga nan ya je nahiyar Turai da sana'ar tamaula.

Shi ne ya bai wa Rashidi Yakini, kwallon da Najeriya ta fara ci a gasar kofin duniya a karawa da Bulgaria a Amurka ranar 19 ga watan Junin 1994.

Aikin da aka bai wa George shi ne ya kai Super Eagles gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Canada da kuma Mexico.

Kenan ya zama wajibi Najeriya ta doke Afirka ta Kudu a Uyo da kuma Jamhuriyar Benin a Abidjan a wasannin neman shiga gasar kofin duniya da suke gabanta.

Super Eagles tana ta uku a rukuni na uku a neman gurbin shiga gasar kofin duniya, biye da Rwanda da kuma Afirka ta Kudu.

Haka kuma Najeriya na fatan shiga gasar kofin Afirka da za a yi a Morocco a 2025.


No comments