Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ayyukan Gwamnatin Neja Matasa Za Su Ci Moriyarsa

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar ayyukan raya kasa da gwamnatin Manomi Gwamna Umar Mohammed Bago ta sanya a gaba matasa ne zasu ci...


Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar ayyukan raya kasa da gwamnatin Manomi Gwamna Umar Mohammed Bago ta sanya a gaba matasa ne zasu ci moriyarsa. Kodineta a bangaren wayar da kai, Hon. Abubakar Haruna (T/Black) ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Minna.

Abubakar Haruna, ya cigaba da cewar tun dawowar mulkin dimukuradiyya jihar Neja ba ta samu zakakumin gwamna irin Umar Bago ba, musamman yadda ya rungumi matasa ya sanya su cikin gwamnati inda ya ba su mukamai masu tsoka dan tafiya da kowa ta yadda wadanda suka wahala a siyasa ba su ce an yi watsi da su ba.

Yanzu idan ka duba ayyukan raya kasa daruruwan matasa ne ke anfana wajen samun kudaden biyan bukatun yau da kullum, musamman a karamar hukumar Chanchaga inda gwamnati ta kuduri aniyar yin hanyoyi sama da dari wadanda yanzu haka duk mazauna Minna fadar gwamnatin jiha shaida ne tun bayan kama madafun ikon jihar nan.

Yanzu bisa kididdiga ba za ka iya bada adadin matasan da ke ayyukan karfi ba wadanda a kullun ake biyan su kudaden ayyukan da su kayi na gina magudanan ruwa, da matasan da hukumar kula da tsafta (NISEPA) ta dauka aikin sharar magudanan ruwa ba sa kirguwa.

Saboda idan jama'a musamman matasa suka cigaba da baiwa gwamnati goyon baya damar su zasu rabu da radadin rashin aikin yi da yaki da zaman kashe wando, ina jadadda goyon bayan matasan Chanchaga da jihar Neja wajen ganin gwamnatin nan ta cin ma kudurorinta.

Jama'iyyar APC, jam'iyya ce ta talakawa kuma gwamnatin Bago ta kudurin aniyar samar da sabuwar jihar Neja wadda muka dade muna mafarkinsa a jihar nan, musamman wajen farfado da tattalin arzikin jihar da bunkasa harkar noma da itace hanyar da mutanen karkara suka dogara akan sa.

Matsalar tsaro da muka dade muna fama da ya daidaita mutanen karkara, da yardar Allah nan bada jimawa ba zai zama tarihi wanda zai karfafi guiwar manoman mu ta yadda za mu iya noman abincin da za mu iya fitarwa kasashen ketare.

No comments