Daga Awwal Umar Kontagora Shugaban kungiyar leburori masu hakar ma'adanan kasa ( Nigeria Union Of Miner Workers) ta gargadi yayan kungiy...
Daga Awwal Umar Kontagora
Shugaban kungiyar leburori masu hakar ma'adanan kasa ( Nigeria Union Of Miner Workers) ta gargadi yayan kungiyar da su guji taka dokar gwamnatin jiha na dakatar da hakar ma'adanai a jihar, domin uwar kungiya ta jiha karkashin jagorancin Comr. Musa Adamu Nasko ta nuna biyayyarta ga gwamnati wajibi ne mu kan a matakin karamar hukuma mu zama masu biyayya ga dokar.
Shugaban a karamar hukumar Paikoro, Malam Mustapha Abdullahi ne yayi jan kunnen bayan kammala wani zama da yayan kungiyar da ya gudana yammacin alhamis din makon nan a garin Paiko fadar karamar hukumar.
Ya cigaba da cewar muna aiki kafada da kafada da jami'an tsaro da sarakunan gargajiya, duk wanda yayi kunnen uwar kashi ya bari ya shiga hannu to ya kuka da kan sa.
Malam Mustapha ya koka kan halayan wasu yayan kungiyar na yin watsi da ayyukan raya kungiya, wanda kungiya ba ta cigaba muddin ba a samu hanyar samun kudaden shiga ba, wanda yace dole kowa ya rika bada gudunmawarsa na aljihu da lokacinsa ta yadda idan gwamnati ta janye dokar da ta sanya za a samu cigaban da kowa zai anfana.
NUMW ba kungiya ce ta kara zube ba, kungiya ce da gwamnati ta amince da ita kuma take hadin guiwa da kungiyar kwadago ta kasa, wajibi ne mu nuna jajircewar mu wajen gina wannan tafiyar hakan ne zai baiwa uwar kungiya kwarin guiwa na amincewa da mu, domin daga shigar NUMW mun samu cigaba a wannan harkar kamar yadda muke samun hadin kan jami'an tsaro wajen ba mu kariya da samun tagomashi wajen sarakunan gargajiya, muna da kwarin guiwa idan gwamnati ta kammala tsare tsaren ta za mu samu yancin gudanar da ayyukan mu yadda ya dace bisa dokar da gwamnatin jiha ta aminta da shi.
Da yake karin haske, ma'ajin kungiyar Malam Abubakar Musa yace kudaden shiga kungiyar ya ja baya wanda tilas duk wanda ke da rajista da kungiya ya tabbatar yana biyan kudaden shi kamar yadda aka tsara domin akwai ayyuka da dama a gaba, kuma da kudaden da ke shigowa ne kawai za a iya aiwatar da su.
Koda mutum ba zai samu damar zuwa taron kungiya ba wajibi ne ya rika aiko da kudin shi tare da sanar da kungiya dalilansa na rashin samun damar halartar taron tun lokacin taro, dan haka za mu cigaba da wayar da kan yayan kungiya muhimmancin wannan tafiyar da kuma alfanun da muke sa ran samu nan gaba kadan.
Kungiyar ta bi sahun uwar kungiya ta jiha bisa tangwa da rarrashin gwamnatin jiha wajen sakar masu mara dan cigaba da aikin su ganin ba a taba samun wani laifi ko cin zarafin al'umma da sunan aikin ma'adani ba.
Aikin hakar ma'adanai a jihar Neja ya tsaya tsawon lokaci bisa umurnin dakatarwar da maigirma Manomi gwamna Umar Mohammed Bago ya bayar wanda ya jefa dubban masu aikin hakar ma'adanai, daga kan leburori zuwa yan kasuwa da masu kamfanoni cikin wani hali zuwa yanzu.
No comments