Tsohon Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya shaidawa daruruwan magoya bayan sa da suka yi cincirindo a kofar gidan sa cewar an take...
Tsohon
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya shaidawa daruruwan magoya bayan sa
da suka yi cincirindo a kofar gidan sa cewar an take masa hakkokin sa a daidai
lokacin da wa’adin kotu na ganin ya gabatar da kan sa a gidan yari ke cika yau
lahadi, inda yake cewa ba zai gabatar da kan sa ba.
Zuma
yace alkalan kotun kasar sun take masa hakkokin sa wajen yanke masa hukuncin
tasa keyar sa zuwa gidan yari na watanni 15 saboda kin bada shaida a gaban
kwamitin dake gudanar da bincike akan zargin cin hanci da rashawa da ake masa.
Magoya
bayan tsohon shugaban sun sha alwashin jefa Afirka ta kudu cikin rudani muddin
aka jefa Zuma gidan yari kamar yadda kotu ta bada umurni.
Yau
lahadi wa’adin kwanaki 5 da aka baiwa Zuma ya gabatar da kan sa a gidan yari ke
cika, amma ya zuwa wannan lokaci babu alamar cewar zai mutunta umurnin.
A
wani yunkuri na tauna tsakuwa, magoya bayan tsohon shugaban sun yi gangami a
kofar gidan sa dake Nkandla a Yankin KwaZulu Natal domin hana duk wani yunkuri
na tura shi gidan yari.
Yayin
jawabi ga magoya bayan sa, Zuma yace yadda ya ga Yan Sanda yana mamakin yadda
zasu iya kaiwa gare shi wajen kutsawa a tsakanin daruruwan mutanen da suka yi
gangami a kofar gidan sa domin kama shi.
Wani
mai goyan bayan sa Lindokuhle Maphalala ya shaidawa kamfanin dillancin labaran
Faransa cewar, koda ministan Yan Sanda Bheki Cele yaje gidan Zuma sai dai ya
fara da kama su kafin kaiwa ga tsohon shugaban.
Wasu
daga cikin jama’ar dake wurin sun bukaci shugaba Cyril Ramaphosa da ya sauka
daga mukamin sa, yayin da suka yi alkawarin cewar daga gobe litinin zasu hana
ruwa gudu a fadin kasar.
No comments