Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewar ‘yan bindigar dake garkuwa da mutane a jihar sun hallaka mutum bakwai da suka kama a kananan hukum...
Gwamnatin
jihar Kaduna ta bayyana cewar ‘yan bindigar dake garkuwa da mutane a jihar sun
hallaka mutum bakwai da suka kama a kananan hukumomin Chikun da Kajuru da kuma
Giwa.
Kwamishinan
tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana haka sakamakon rahotannin
da ya samu daga hukumomin tsaron jihar.
Aruwan
ya ce rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kashe mutane 4 da suka kama a kusa da
Tsohon Gayan dake karamar hukumar Chikun, yayin da 2 daga cikin su suka fito
daga kauyen Kakau, guda kuma ya fito daga Kachia sai kuma na 4 da ba a iya
tantancewa ba.
Sanarwar
kwamishinan ta ce an kashe kuma mutane 2 a Tashar Iri dake karamar hukumar
Kajuru, sai kuma guda a tsohon Farakwai dake Igabi.
Aruwan
ya ce Gwamna Nasir El Rufai ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda aka
kashe.
No comments