Rahotanni sun bayyana cewa wadansu ƴan bindiga sun afka gidajen ma’aikatan asibitin Kutare a garin Zaria suka yi awon gaba da mutum 15...
Rahotanni sun
bayyana cewa wadansu ƴan bindiga sun afka gidajen ma’aikatan asibitin Kutare a
garin Zaria suka yi awon gaba da mutum 15.
Wani ma’aikacin asibitin ya shaida wa BBC cewa
mutanen da ƴan bindigar suka sace sun ƙunshi maza da mata da kuma ƙananan yara.
Ya ce an ƴan bindigar sun kai harin ne tsakiyar dare
zuwa wayewar safiyar Lahadi.
Wasu rahotanni sun ce cikin mutanen da ƴan bindigar
suka yi garkuwa da su har da jarirai.
Zuwa yanzu gwamnatin Kaduna da rundunar ƴan sandan
jihar ba su fitar da sanarwa ba game da harin.
No comments