Madogara ta nakalto daga kafar watsa labarai ta Rfi Hausa cewa; firaministan rikon kwarya na Haiti Claude Joseph ya tabbatar da yiwa shuga...
Madogara
ta nakalto daga kafar watsa labarai ta Rfi Hausa cewa; firaministan rikon
kwarya na Haiti Claude Joseph ya tabbatar da yiwa shugaban kasar Jovenel Moise
kisan gilla a gidansa yau laraba, yayin wani farmaki da ya kai ga jikkata
matarsa.
Kisan
gillar ga shugaba Jovenel Moise ya sake tabbatar da hadari baya ga karuwar
matsalar tsaron da kasar ta yankin Caribbean ke gani da kuma rikicin siyasar da
ya dabaibayeta a bangare guda kuma aikin garkuwa da mutane na ci gaba da
tsananta.
A
jawabin da ya gabatar lokacin kadan bayan kisan shugaban, Firaministan rikon
kwaryar na Haiti Claude Joseph ya ce yanzu shi ne zai ci gaba da jan ragamar
kasar, yayinda ya roki al’ummar kasar da su kwantar da hankulansu yana mai cewa
jami’an tsaro na daukar matakan da suka dace don tabbatar da tsaron al’umma.
Kalaman
na Joseph ya bayyana cewa mutanen da suka yiwa shugaban kisan gilla baki ne da
suka shiga kasar, kuma bayanai sun nuna suna magana ne da turancin Ingilishi da
kuma Spaniyanci.
Haiti
da ke matsayin matalauciyar kasar a kaf takwarorinta na nahiyar Amurka, shugaba
Moise ya dauki tsawon lokaci y ana mulki, duk barazana da kuma bukatar ajje
mukaminsa.
Baya
ga zaben kasar da coronavirus ta tilasta dagewa Haiti kuma na shirin yiwa
kundin tsarin mulkinta kwaskwarima nan da watan Satumba.
Tuni
dai shugabannin kasashe suka fara aikewa da sakon ta’aziyya ciki har da
Firaminista Boris Johnson yayinda Jamhuriyyar Dominica ta sanar da kulle
iyakokinta da kasar.
No comments