Da sDa sanyin safiyar yau ne mutanen Kauyen Garka cikin su ya duri ruwa bayan wani hari da mayakan Boko Haram suka kai Kauyen Dabna da ke ...
Da sDa sanyin safiyar yau ne mutanen Kauyen Garka cikin su ya duri ruwa bayan wani hari da mayakan Boko Haram suka kai Kauyen Dabna da ke Karamar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa.
Mazauna Kauyen Garka, inda Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya fito, suna cikin razani bayan samun labarin kawo musu hari da mayakan Boko ke shirin yi.
Shi dai wannan rahoton na zuwa ne bayan kisan gillar da ’yan ta’addan suka yi wa mutum 18 a kauyen Dabna da ke makwabtaka da su.
Mun samu labarin faruwar lamarin da safiyar ranar Laraba, inda wani mazaunin kauyen ya ce jama’a da dama sun yi kaura zuwa wasu kauyukan da ke makwabtaka da su domin ceton rai.
Wani da ya tsallake rijiya da ya baya, Hilda Joshua, ya ce baya ga wadanda aka kashe, mutane da dama sun jikkata yayin harin da mayakan suka kai. Kamar yadda ya ce da kyar ya samu ya tsere cikin jeji amma akwai ’yan uwansa da dama da kuma makota da abin ya rista da su a kauyen.
Haka kuma, wata majiyar ta bayyana cewa, bayan mutanen da aka kashe a cikin kauyen, ya kuma ga gawawwakin mutum uku a cikin dajin Kwapre da ke kusa da su.
Wasu majiyoyin sun ce, wani jirgin yaki na dakarun soji ya rika kai komo a sararin samaniyar kauyen domin mayar wa maharan martani.
Sai dai an nemi a jin ta bakin Mai Magana da Yawun rundunar sojin yankin, Manjo Muhammad Haruna, ya ci tura, a yayin da wakilanmu basu samu layin wayarsa ba a lokacin hada wannan rahoto.
No comments