Daga BBC Hausa Majalisar Dokokin Jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya ta dakatar da shugaban Hukumar Karɓar ƙorafe-ƙorafe da cin hanc...
Majalisar Dokokin Jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya ta dakatar da shugaban Hukumar Karɓar ƙorafe-ƙorafe da cin hanci da rashawa ta jihar KPCACC, Muhuyi Magaji Rimin Gado, na tsawon wata guda.
A zaman da ta yi a ranar Litinin ne majalisar ta ce ta dakatar da Muhuyi, saboda wani ƙorafi da ta samu a kansa daga ofishin Babban Akanta na jihar ta Kano.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano Labaran Abdul Madari ya shaida wa BBC cewa an dakatar da Muhyi Magaji ne saboda ƙin amincewa da akanta da aka aika masa daga ofishin babban akatna jihar.
Sai dai Muhuyi ya yi watsi da wannan zargi a wata hira da BBC ta yi da shi a baya-bayan nan.
n daɗe ana yi wa Muhuyi kallon mutum mai yawan jawo ce-ce-ku-ce kan abubuwa da dama a jihar Kano.
Bari mu ɗan yi waiwaye kan waye Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Wane ne Muhuyi Magaji?
Muhuyi Magaji wani ɗan siyasa ne kuma ɗan gwagwarmaya mai rajin yaƙi da cin hanci da rashawa a jihar Kano.
A lokacin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau tsakanin 2003 zuwa 2011 yayin da Muhuyi yake matsayin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Rimin Gado, ya taɓa kai ƙorafi ga hukumar EFCC ta ƙasa kan wasu kuɗaɗen ƙaramar hukumar da suka maƙale.
A lokacin da kuɗin suka fito yana riƙon shugabacin ƙaramar hukumar, kasancewar shugaban ƙaramar hukumar ya yi tafiya. Kuma nan take ne ya fara gudanar da wasu ayyukan ci gaba da kuɗaɗem a ƙaramar hukumar, lamarin da ya ja babu shiri shugaban ƙaramar hukumar ya dawo daga wata tafiyar da ya yi.
Wannan abu ya jawo saɓani tsakaninsa da shugaban ƙaramar hukumar ta Rimin Gado. Lamarin nan ya fara fito da Muhuyi a idon al'umma a matsayin mai yaƙi da cin hanci da rashawa.
Ya taɓa dakatar da rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi na riƙo a jihar Kano bayan da ya kai ƙorafi kotu, lokacin dai da yake matsayin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar.
Bayan da Gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso ya koma mulki a shekarar 2015, Muhuyi ya zama jami'in ƙaramar hukuma na farko da ya mayar da motar gwamnati, wanda hakan ya tilasta wa sauran shugabannin ƙananan hukumomi mayar da nasu.
Ya ce ya yi hakan ne don tsayawa a kan gaskiya. Sai dai hakan ya jawo masa matuƙar baƙin jini a wajen takwarorinsa a lokacin.
Ya kafa wata ƙungiya mai zaman kanta wacce ke yaƙi da cin hanci da rashawa, kuma bayan nan ne Gwamna Abdullahi Umar ganduje ya naɗa shi shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rahswa ta jihar Kano a shekarar 2016.
A lokacin da yake riƙe da wannan muƙami ya janyo ce-ce-ku-ce sosai inda ya dinga rigima da ɓangarori daban-daban.
Ya yi rigima da ma'ikatan kotu, ya binciki alƙalai, ya binciki manya-manyan ƴan siyasa, ya binciki Masarautar Kano har sau biyu duk kan zargin almundahana da ɓarnata kudaɗen gwamnati.
A lokacin da yake shugabantar hukumar ya koma ya yi karatun shari'a inda ya zama lauya.
Wasu masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun ce Muhuyi ya matukar ɗaga darajar hukumar ta cin hanci da rashawa ta jihar Kano, har ta zama hukumar da jami'an gwamnati da attajirai da 'yan kasuwa da sarakai suke tsoronta.
Sai dai wasu na yi masa zargin cewa ana amfani da shi don cimma wasu burikan siyasa, zargin da ya sha musantawa inda yake cewa yana aikinsa tsakaninsa da Allah.
A yanzu za a zuba ido a ga mai zai faru tsakanin Muhuyi Magaji da Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Dalilan Da Suka Sa Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Sauke Shi
Shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Labaran Madari ne ya nemi kwamitin yaƙi da cin hanci da rashawa na majalisar ya ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin
No comments