Majalisar dokokin Nijeriya ta amince da sabuwar dokar hakar man fetur da iskar gas da aka kwashe sama da shekaru 20 ana tafka mahawara a...
Majalisar dokokin Nijeriya ta amince da sabuwar
dokar hakar man fetur da iskar gas da aka kwashe sama da shekaru 20 ana tafka
mahawara akai ba tare da cimma matsaya ba.
Sabuwar dokar wadda ake saran za ta bude kofar zuba
jari daga masu ruwa da tsaki akan harkar mai da iskar gas za ta kuma bada damar
sake fasalin raba arzikin da ake samu daga bangaren tattalin arzikin musamman
ga yankunan da ake aikin hako man.
Shugaban kwamitin man fetur a Majalisar wakilai
Mohammed Manguno ya gabatar da tanade-tanade 319 dake cikin sabuwar dokar kafin
Majalisar ta amince da ita.
Shugaban Majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya
yabawa ‘yan Majalisu saboda gagarumin aikin da suka yi wajen amincewa da
sabuwar dokar wadda ya ce za ta taimaka wajen daga darajar Nijeriya.
Shima shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya
jinjinawa ‘yan Majalisun saboda amincewa da sabuwar dokar.
Majalisun da suka gabata sun yi ta kokarin sake
fasalin dokar na man fetur amma kokarin su ya gaza cimma ruwa.
No comments