Hadin gwuiwar rundunar sojojin kasashen Afirka ta Yamma ta yi nasarar kashe mayakan Boko haram 13 a fafatawar da suka yi da su a kudu maso...
Hadin gwuiwar rundunar
sojojin kasashen Afirka ta Yamma ta yi nasarar kashe mayakan Boko haram 13 a
fafatawar da suka yi da su a kudu maso gabashin kasar, abin da ya kai ga kashe
fararen hula guda 4.
Sanarwar da dakarun
suka gabatar ta ce mayakan a cikin motoci goma sun yiwa sojojin kwantar bauna
ne yammacin talata akan hanyar Diffa
zuwa Maine Soro amma sai yunkurin na su ya kasa cimma biyan bukata inda sojojin
suka bude musu wuta.
Rahotanni sun ce kafin
harin, mayakan sun tare wata motar safa daga bisani kuma suka kai hari akan
wasu mazauna kauye inda suka kashe mutane 4, cikin su harda direban motar da
Sarkin kauyen.
Sanarwar sojin tace
dakarun su guda 4 sun samu raunuka a fafatawar da suka yi, yayin da su kuma
suka kashe mahara 13 daga cikin su da kuma kwashe makamai da motar su guda.
Mayakan boko haram dake
dauke da makamai sun zafafa kai hare hare a Diffa dake Jamhuriyar Nijar kusa da
Yankin Tafkin Chadi tun daga watan Mayu.
Ko a watan jiya mutane
kusan 6,000 da suka tsere daga garuruwan su sakamakon karuwar hare hare a Yankin
sun fara komawa garuruwan su.
Akalla mutane 300,000
da suka fito daga Najeriya da Nijar ke zaman gudun hijira a Yankin Diffa abin da
ya sa shugaban kasa Bazoum Mohammed ya kaddamar da shirin mayar da su garuruwan
su.
No comments