Rfi Hausa ta labarto cewa; hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda tashin farashin kayan abincin ke kokarin ninka yawan...
Rfi
Hausa ta labarto cewa; hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta koka da
yadda tashin farashin kayan abincin ke kokarin ninka yawan yunwar da ta yi
hasashen za a gani cikin shekarar nan.
Alkaluman
da hukumar ta fitar ya nuna cewa, farashin kayan abincin a baya-bayan na tashi
cikin sauri a kusan dukkan sassan Duniya, cikin wani yanayi da ba a taba gani ba
a shekaru 10 da suka gabata.
A
cewar hukumar ta FAO annobar covid-19 ta taimaka matuka wajen kara karanci da
kuma tsadar abinci a sassan Duniya da akalla kashi 40 wanda ke matsayin tashi
mafi tsanani da aka gani tun bayan shekarar 2011.
Shugaban
sashen tattalin arziki na FAO Arif Husain ya ce farashin masara ya karu da
kashi 88 yayinda waken suya ya karu da kashi 73 kana kayan abinci nau’ikan
hatsi da mayukan girki ya karu da kashi 38 kana sukari da kashi 34 sai nama da
kashi 10, alkaluman da jami’in ke cewa barazana ce ga tattalin arzikin Duniya.
Bayanai
na nuna tashin farashin kayan da irin wanda aka gani a shekarar 2007 zuwa 2008
da kuma shekarar 2010 zuwa 2011 lokacin da kasashen Larabawa suka yi boren
sauyin gwamnati da ya haddasa rikici tare da karancin abinci a yankuna
daban-daban an Duniya.
Hukumar
ta ce duk lokacin girbi zai bayar da damar sassautowar farashin kayakin, amma
alamun na nuna abu ne mai wuya farashin ya dawo kamar baya a cikin sauki,
la’akari da yadda annobar covid-19 ta shafi tattalin arzikin kasashe tare da
takaita harkokin noma a yankuna da dama.
Haka
zalika, hukumar ta FAO ta ce matsalar dumamar yanayi ta taimakawa wajen haddasa
karancin abinci sakamakon fuskantar ambaliyar ruwa ko kuma jinkirin faduwar
damuna a yankunan da suka dogara da ruwan sama wajen noma.
Hukumar
ta FAO ta ce Lebanon ce kan gaba a jerin kasashen da za su fuskanci ko kuma su
ket saka da fuskantar matsalar ta karancin abinci inda farashin kayaki suka
ninka zuwa kasha 226.
Sauran
kasashen sun hada da Argentina, da Najeriya inda cikin kankanin lokaci mutane
miliyan 7 suka fada cikin talauci tukuna daidakun kasashen Afrika da Asiya da
kuma latin Amurka.
No comments