Gwamnatin Nijeriya ta ce jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB mai neman kasar Biafra Nnamdi Kanu, ya haddasa kashe mutane akalla 60 tare da...
Gwamnatin Nijeriya ta ce jagoran haramtacciyar
kungiyar IPOB mai neman kasar Biafra Nnamdi Kanu, ya haddasa kashe mutane
akalla 60 tare da lalata dukiya mai yawan, yayin hare-hare fiye da 50 da
mabiyansa suka kai a sassan yankin kudu maso gabashi da kuma kudu maso kudancin
kasar.
Daga cikin jerin ta’adin Nnamdi Kanu da gwamnatin
Najeriya ta zayyana cikin wasikun da ta aikewa jakadun kasashen yammacin Turai
akwai hare-haren da mabiyansa suka kai tsakanin 26 watan Janairu zuwa 19 ga
Afrilun da ya gabata a jihar Abia inda suka kasha ‘yan sanda 6, sai a Akwa Ibom
inda ‘ya’yan haramtacciyar kungiyar IPOB suka kashe mutane 25 ciki har da
jami’an tsaro yayin hare-haren da suka kaddamar a sassan jihar tsakanin 27 ga
watan Janairu zuwa 19 ga watan Afrilu.
Wasikar gwamnatin Najeriya ta kara da cewar mabiyan
Nnamdi Kanu sun kuma kashe ‘yan sanda da soja daya a jihar Cross River a farkon
watan Maris, yayin da kuma tsakanin watan Janairu zuwa tsakiyar Afrilu, suka
kasha mutane 11 ciki har da jami’in tsaro a garin Onitcha dake jihar Delta.
WASIKAR
GWAMNATIN TARAYYA
Aikewa da wasiku zuwa ga Jakadun kasashen yammacin
Turan kan ta’adin mabiyan Nnamdi Kanu ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Nijeriya
ke bayyana damuwa kan yadda hukumomin wasu kasashen ketaren ke goyon bayan masu
tayar da kayar bayan masu neman ballewar da suke yi, ta hanyar baiwa jagoran
nasu damar watsa shirye-shiryen tunzura barkewar rikici ta kafar rediyo.
TSEREWAR
KANU
Kanu da ya tsere daga Nijeriya a shekarar 2017 bayan
belin shi da kotu ta bayar, ya sake gurfana gaban babbar kotun Nijeriya dake
Abuja a ranar Talata, bayan kamo shi da jami’an tsaron Nijeriya suka yi daga
ketare.
No comments