Daga Idris Umar Kaduna Ƙungiyar matan shugabannin Kananan hukumomi na jihar Kaduna sun ziyarci Mataimakiyar Gwamnan jihar Kaduna...
Daga Idris Umar Kaduna
Ƙungiyar matan shugabannin Kananan hukumomi na jihar Kaduna sun ziyarci Mataimakiyar Gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa.
Uwargidan shugaban Ƙungiyar kananan Hukumomin jihar Kaduna ALGON ne ta jagoranci tafiyar ta su.
Kamar yadda shugaban kungiyar kuma matar shugaban ALGON, Honorabul Liman Abubakar Buba ta sanar cewa wannan ziyara ta kumshi ta sada zumunci ne da neman goyan baya ga ƙungiyar matan shugabannin kananan hukumomi na jihar Kaduna, haka zalika matan sun roki arzikin karfafa harkokin mata da matasa a jihar ta su baki daya kamar yadda mataimakiyar gwamnan ta wallafa a shafinta na Facebook.
No comments