Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar a matsayin Ministan Tsaro, yayin da ya nada tsohon gwamna...
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar a matsayin Ministan Tsaro, yayin da ya nada tsohon gwamnan Riverrs Nyesom Wike a matsayin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, inda kuma Festus Keyamo aka nada shi a matsayin Ministan Sufurin Jiragen Sama.
Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Ajuri Ngelale ne ya tabbatar da mukamman a wannan Larabar.
Ga sauran ministocin da mukammansu
Daga yankin arewa maso yammacin Najeriya
Hannatu Musawa - Ministar Raya Al'adu
Bello Matawalle - Karamin Ministan Tsaro
Yusuf T. Sunumu -Karaminin Ministan Ilimi
Ahmed Dangiwa - Ministan Gidaje da Raya Birane
Abdullahi Gwarzo - Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane
Atiku Bagudu - Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki
Kaduna - Ministan Muhalli
Mairiga Mahmud- Karamar Ministar Abuja
Bello Goronyo - Karamin Ministan Albarkatun Ruwa da Tsafta
Abubakar Kyari - Ministan Noma da Tsaron Abinci
Tahir Momoh - Ministan Ilimi
Sa'idu Alkali - Ministan Cikin Gida
Yusuf Tugga - Ministan Harkokin Waje
Ali Pato - Ministan Tsare-tsaren Kiwon Lafiya da Ci gaban Al'umma
Ibrahim Gaidam - Ministan 'Yan sanda
U Maigari Ahmadu - Karamin Ministan Bunkasa Albarkatun Karafa
Daga yankin Arewa ta Tsakiya
Shu'aibu Audu - Ministan Bunkasa Albarkatun Karafa
Muhammed Idris - Ministan Yada Labarai
Lateef Fagbemi - Ministan Shari'a
Simon Lalong - Ministan Kwadago
Imam Suleiman Ibrahim - Karamin Ministan 'Yan sanda
Zephianiah Jisalpo - Ministan Ayyuka na Musamman
Joseph Utsev - Ministan Albarkatun Ruwa da Tsafta
Aliyu Sabi Abdullahi - Karamin Ministan Noma da Tsaron Abinci
Abubakar Momoh - Ministan Matasa
Betta Edu - Ministar Jin-kai da Rage Radadin Talauci
Ekperikpe Ekpo - Karamin Ministan Albarkatun Iskar gas
Heineken Lokpobiri - Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur
John Enoh - Ministan Wasanni
Sauran Ministocin da mukamansu
Bosun Tuani - Ministan Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Zamani
Ishak Salako - Karamin Ministan Muhalli
Wale Edun - Ministan Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki
Bunmi Tunji-Ojo - Ministan Harkokin Ruwa
Adebayo Adelabu - Ministan Wutar Lantarki
Tunji Alausa - Karamin Ministan Lafiya da Walwalar Al'umma
Dele Alake - Ministan Albarkatun Karkashin Kasa
Lola-Ade John - Ministar Yawon Bude Ido
Adegboyega Oyetola - Ministan Sufuri
Doris Anite - Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari
Uche Nnaji - Ministan Kirkire-kirkire, Kimiya da Fasaha
Nkiruka Onyejeocha - Karamar Ministar Kwadago
Uju Kennedy - Ministar Mata
David Umahi - Ministan Ayyuka
Ekperipe Ekpo - Karamin Ministan Albarkatun Iskar gas
No comments