Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Nemi Gwamnati Ta Binciki Masu Rike Da Mukamai Fiye Da Daya, In ji Danjuma Masu

Daga Awwal Umar Kontagora An nemi gwamnatin Neja da tabbatar ta binciki masu rike da mukamai fiye da daya tare da tabbatar da ta karbe domin...


Daga Awwal Umar Kontagora

An nemi gwamnatin Neja da tabbatar ta binciki masu rike da mukamai fiye da daya tare da tabbatar da ta karbe domin bai wa wadanda suka dace. Wani jigon siyasa kuma mai gwagwarmayar ganin matasa sun dogara da kafarsu, Hon. Danjuma Masu ne yayi kiran lokacin da yake nuna farin cikinsa na cikar gwamnatin shekara daya kan madafun iko a jihar Neja.

Hon. Masu, ya cigaba cewar nasarar gwamnatin Bago na shekara daya yafi karfin kasawa akan faranti dan fayyace su, domin ban da ayyukan hanya da tsawon shekaru ashirin da biyar da jihar Neja ke bukatar su, mu a Neja za mu bayyana cewar shekara daya ke nan da fara mulkin dimukuradiyya domin a wannan shekarar ne muka gamsu da cewar an fara gudanar da mulkin dimukurayya.

Idan ka dubi bangaren aikin hanyoyi a jihar Neja ko makaho ya shaidi cewar an samu gwamnatin da ta san abinda take yi, balle maganar kiwon lafiya, wanda tun lokacin mulkin marigayi Shehu Shagari da aka sanya harsashen gina asibitin kwararru da yanzu ya zama kango, hotel din Shiroro gwamnatin Bago ta yi nisa da aiki a wurin dan samar da babban asibitin kwararru da zai kafada da kafada da manyan asibitocin da muke alfahari da su a kasar nan.

Idan ka koma bangaren ilimi, zuwan gwamnatin nan mai alkibla, an samar da jami'ar ilimi cikin dan kankanin lokaci, wanda hakan zai taimaka wajen samun kwararrun malamai da karin yawan likitoci a jihar nan.

Hon. Masu, ya cigaba da cewar maganar rashin aikin yi, yanzu kam manomi gwamna Umar Bago ya rufe mana baki, domin a karamar hukumar Chanchaga kawai fadar gwamnatin jiha, akwai matasa sama da dubu biyu da ke samun naira dubu biyar a kullun sakamakon wadannan ayyukan karfi da aka bude. Dan haka masu kurarin cewar gwamnatin ta bullo da shirin horar da matasa sana'o'in hannu, ban gam su da su ba domin a baya an gabatar da shiraruwa da dama dan matasan amma a karshe idan sun kammala an sallame su, nan take suke sayar da kayan tallafin da aka ba su.

Idan ma gwamnatin na da shirin hakan, to a dubi yaran da iyayen su suka kai wuraren koyon sana'a kuma suka tsaya da gaske suna yi a tallafa masu domin sun nuna da gaske suke, na biyu kuma in ba tallafin karatun kimiyya da fasaha ba, a mayar da hankali a bangaren kiwon lafiya da gaske.

Dan siyasar yace akwai bukatar a waiwayi tsarin makaratun kimiyya da fasaha da horar da sana'o'in hannu ta yadda idan yaro ya taso ya kammala karatunsa zai zama ya taso da sana'arsa.

Jigon siyasar, ya yabawa gwamnatin jiha bisa hubbasar da tayi wajen sayo motoci masu sulke dan karfafa guiwar jam'an tsaro, wanda wannan babban nasara ne a jihar nan, ko ba komai tun bayan zuwan bawan Allah nan bai runtsa ba akan maganar tsaro, sanin kowa ne a samu cigaba sosai, wanda idan al'ummar jiha zasu cigaba da addu'o'in alheri ga gwamnatin da jami'an tsaro za a ci galaba akan yan ta'adda.

Ina jadadda kira na ga hadimin al'umma manomi gwamna Umar Bago, da yasa a yi kyakkyawar bincike, duk dan siyasar da ya rike appointment fiye da daya, ma'aikaci ne ko dan siyasa da a tabbatar an karbe dan baiwa wadanda suka cancanta.

Rahotanni sun tabbatar mana da cewar akwai dan siyasar da aka baiwa damar kawo mutane ashirin, ya dauko makusantan shi, an tantance bayan bude asusun ajiya da ake biyan su albashin wata - wata, ya karbe ATM din su a duk lokacin da albashin ya shigo shi yin sama da kaso mafi tsoka yana tsakura masu abinda ya ga dama.

Maigirma gwamna ya kirkiro wannan appointment din ne dan saka ma wadanda suka wahala da siyasar, amma wasu sun yi awon gaba suna abinda suka ga dama. Wanda wannan laifi ne kuma rashin adalci ne, ba mu taba samun gwamnatin da tayi ruwan appointment kamar gwamnatin Umar Bago ba, gwamnati ta bada appointment sama da dubu takwas, jam'iyyar APC ta bada sama da dubu bakwai kuma wannan an yi shi ne dan cigaban al'ummar jiha, muna zaune gwamna ya ware biliyan ashirin da biyar dan biyan yan fansho.

Shi yasa tun farko na ce nasarorin gwamnatin nan na shekara daya yafi karfin a kasa a tire, domin wanda yasan inda aka fito jiya da inda aka tsaya yau ne kawai zai fahimci abinda ake nufi, duk wadannan nasarorin kyakyawar manufa da kudurin cigaban jihar nan da ke cikin zuciyar maigirma gwamna manomi Umar Bago.

Saboda ina jawo hankalin al'ummar jiha da muka hakuri da irin abubuwan da suka faru kafin zuwan gwamnatin nan, mu taimaka masa da addu'o'i da goyon baya, jihar Neja za ta zama abin koyi da alfahari ga sauran jahohin kasar nan.

Arewa mun yi nisa, shugabannin mu sun yi bacci da yardar Allah idan matasa masu kishi da kyakkyawar manufa kamar Rt. Hon. Umar Bago suka karbi kasar a gaba, zamu samu cigaban da ba a yi tsammani ba.

No comments