Sarkin Zazzau, Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli ya bayyana cewa samun jami’ar kamar Northeaster University dake Gombe a arewa maso g...
Sarkin Zazzau, Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli ya bayyana cewa samun jami’ar kamar Northeaster University dake Gombe a arewa maso gabashin Nijeriya, tabbas zai rage wa iyaye su rika daukar ‘ya’yansu suna kai wa kasashen waje domin karatu.
Sarkin ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kai jami’ar a kwanakin baya. Sarkin har wala yau ya ce tabbas jami’ar ta ginu kuma ta samar da kayayyakin aiki na karatu a tsangayu daban-daban.
Sarkin ya soma da cewa; “Ba ni da wata kalma da zan bayyana irin abubuwan da na gani a wannan jami’a. Akwai jami’o’i da dama masu zaman kansu a Nijeriya, a jihohi daban-daban, amma abin da na gani a wannan jami’a kalmomi sun yi kadan a furta su. Akwai kayan aiki, akwai gine-gine masu kyau. Akwai kayayyakin aiki da suke da shi a dukkanin tsangayoyin karatu, abin alfahari ne ga musamman mutanen arewa.”
Sarkin har wala yau ya ci gaba da cewa; “Zai yi wuya ka je jami’ar da aka tattara dukkanin wadannan kayayyakin aiki da gine-gine a wuri daya kamar wannan jami’a musamman ma ganin yadda yanzu aka fara.
“Ni kaina a matsayina na Chancellor na jami’o’i guda uku; jami’o’i masu zaman kansu da na Tarayya, amma abubuwan da na gani a nan, abin mamaki ne a ce 2022 aka fara wannan jami’a, amma suka cimma wadannan nasarori. Ba abin da za a ce sai dai a taya Sarkin Gombe da wanda ya kafa jami’ar da kuma dukkanin tsangayoyi da kafatanin ma’aikatan jami’ar da masu gudanarwa da kuma jihar Gombe baki daya murna.
“Domin idan akwai irin wannan jami’ar ba abin da zai sa ka kashe kudi ka hau jirgi ka je wata kasa karatu. Hakazalika an rage wa iyaye ko ma nawa ake karba kudin makaranta, tabbas ingantaccen ilimin da ake tunanin za a samu a abin da muka ji muka gani, tabbas za a samu,” ya tabbatar.
“Kuma abin da muke kira ga makarantar nan, su ci gaba da tallata makarantar. Domin ni abin da nake da kiyasi a zuciyata, daga nan zuwa shekara biyu zuwa uku, makarantarnan za ta kasance kusan kowa daga dukkanin sassan Nijeriya za su zo. Za ta zama kamar makarantar Tarayya mai zaman kanta (National Private University). Za ta rika karbar mutane daga ko’ina a Nijeriya”, ya jaddada.
No comments