Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shekara Guda A Mulkin Tinubu: Mece ce Gudunmuwar Kashim Shettima Ga Nasarar Ajandar Sabunta-Fata?

Daga Stanley Nkwocha Shekara  guda ke nan da rantsar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu GCFR wato a ranar 29 ga watan Mayu 2023, kuma nan ta...


Daga Stanley Nkwocha

Shekara  guda ke nan da rantsar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu GCFR wato a ranar 29 ga watan Mayu 2023, kuma nan take ya dauki alwashin samar da sauye-sauyen da za su bayar da sakamakon da zai sauya akalar harkokin mulki a Najeriya. 

Kuma mun gani a kasa, domin a shekara guda na mulkinsa ya kaddamar da kudurorinsa k`ark`ashin taken ajandodi 8 na Sabunta-Fata, wanda suka tafi kafada-da-kafada da alkawuran da ya dauka a lokutan yakin neman zabensa. Wato abin nan da ake kira aiki da cikawa

Duk da abu ne mawuyaci a yi wa gwamnatin da ta gaji tarin matsaloli na shekara da shekaru alkalanci a shekararta ta farko, amma duk da haka za a iya dora manufofin da gwamnatin ta mai da hankali a kansu bisa sikeli don hasaso nasara ko akasinta a turbar da ta hau. Nan ma amsar ita ce Sambarka!

Masu magana kan ce ba a gini bisa tubalin toka. Wannan ita ce Kalmar da ta dace da kiyasin abinda Shugaba Tinubu ya yi a shekara daya na mulkinsa k`ark`ashin Ajandar Sabunta Fata-na gari, a matsayinsa na maginin Sabuwar Najeriya ya san dora gini a kan rusasshen harshashi ba zai taba samar da d`a mai ido ba don haka ya zama dole ya baje turakun tokar da aka shimfida Najeriya a kai ya shimfida mata nagartaccen tubali.

Ba fa kan mu farau ba, kusan duk faÉ—in duniya, gwamnatoci kan ci karo da irin wannan yanayi a shekarun mulkinsu na farko. Abu na farko da ya wajaba ga ko wace sabuwar gwamnati shine kafa sabuwar majalisar ministoci, da za6o nagartattun mutane da za su rike madafun iko a 6angarorin zartarwa. Sai abu na biyu, wanda shine fayyacewa tare da bullo da tsare-tsare na manufofin da za su tafi sau da kafa da abubuwan da suka alkawarta wa al'ummar kasa. Abu na uku, shine kafa tsarin shugabanci bisa doron manufofin da za su dace da manufofin takwarorinsu na kasashen waje

Tun bayan samin `yancin kan Najeriya a shekarar 1960, kasar ke taka rawa sosai a harkokin Afirka da ma duniya baki daya. Hakan ya sa su ma kasashen duniya na sanya manufofi da tsare-tsaren sabbin gwamnatocin Najeriya a faifai a matsayinta na giwar Afirka domin tantance yadda za ta aiwatar da mulkinta, kamar yadda su ma al`ummar k`asa kan sanya idanu kan manufofin kasashen waje da kuma muradun sabbin shugabannin kasar.

A irin wannan yanayi, ba sabon abu ba ne masu taimaka wa shugaban k`asa su yi gudun-wuce-sa'a ta bayan fage don tabbatar da kwazon su a wani aiki ba

Sabanin zarge-zargen da ke shawagi a wasu kafofi cewa wai! An yi watsi da mataimakin shugaban kasar, na san idan da adalci su kansu masu kumfar bakin shaidu ne kan cewa mataimakin shugaban k`asa Sanata Kashim Shettima ya taka rawa a muhimman wuraren da ake bukatarsa. Amma idan sun kasa bayar da shaidar ni zan bigi kirji na tabbatar da wannan ikirarin nawa

Cikin ruwan sanyi VP Kashim Shettima yake samin damar jagorantar manyan aiyukan da a baya wadanda suka ta6a d`ana kujerar mataimakan shugaban k`asa kan same su ne a  mafarki ko kuma bayan sun sha wahala.

 A yayin da Shugaba Tinubu ke mayar da hankali kacokan kan harkokin gudanar da Mulki, mataimakinsa na taimaka masa a bangaren da ya fi kwarewa a fannin farfado da tattalin arzikin Najeriya na gama-gari a matsayinsa na gogaggen masanin tattalin arziki da noma, da sabbin dabarun habaka tattalin arzikin duniya na karni na 21

 A shekararsu ta farko kan karagar mulki, Shugaba Tinubu da VP Shettima sun dukufa wajen tabbatar da mulkin Najeriya, inda suka fuskanci matsaloli da dama musamman a bangaren tattalin arziki, tsaro da walwalar ‘yan kasa. Ajandodi 8 na gwamnatin Tinubu sun samar da tsayayyen tsari ga manufofi shirye-shiryen gwamnatin, tare da mai da hankali kan samar da ayyukan yi, bunkasar tattalin arziki, samar da abinci, kawar da talauci, samun jari, bin doka da oda, yaki da cin hanci da rashawa, da ci gab ana bai daya.

Ko shakka babu, Shugaba Tinubu yana da cikakken masaniya kan kwarewar Kashim Shettima a bangaren jagoranci, shiyasa ma ya zabe shi a matsayin abokin takararsa, kuma ba ya da haufi cewa Kashim ba zai yi k`asa a gwiwa ba a matsayinsa dan gani-kashenin jigo a siyasar Arewa mai mara wa shugaban baya.

Kamar yadda aka zata, mataimaki kuma amintaccen aminin shugaban kasa, ya taimaka wajen aiwatar da manyan sauye-sauyen da gwamnatin Sabunta Fata-na gari ta taso a gaba, tare da daukar matsaya da zartas da hukumci a kan batutuwa masu sarkakiya da suka shafi gudanar da  mulkin kasa, wannan kenan, baya da manyan taruka da shi mataimakin shugaban kasar ke jagoranta a madadin me gidansa a mafi yawan lokuta domin sake farfado da  ruguzajjen tattalin arzikin da suka gada.

Sau da yawa shuwagannin biyu kan yi amfani da kwarewarsu a jagoranci da siyasa don samar da sabon tsarin jagoranci. 

Baki dayan masu lura da al’amuran yau da kullum sun yi amannar cewa mataimakin shugaban k`asa jajirtacce ne kuma ya iya sadaukar da kai wajen tafiyar da ayyuka.

Shugaban da mataimakinsa sun hada karfi da karfe wajen zame wa Najeriya jirgin Annabi Nuhu (AS) don ceto ta daga nutsewa a tekun matsalolin da suka gada. 

Kada na cika ku da surutu, bari na jero wasu daga cikin matakai da ginshikan da suka kafa ya zuwa yanzu:

1. A Bangaren Huldar Diflomasiyar Duniya Da Zuba Jari Na kasashen Waje

Bayan hawansu mulki, shugaba Tinubu da mataimakinsa Shettima sun fara gudanar da manyan ayyuka da suka shafi k`asa da kasa, inda aka yanke shawarwari masu muhimmanci da suka shafi Najeriya da nahiyar Afirka, kuma a mafi yawan lokuta shugaban kan nuna kwarin gwiwa kan  Shettima na iya wakiltar kasar da kyau a ko ina a fadin duniya, ba akan al`amurran da suka shafi matakan da gwamnati ta dauka kad`ai ba har ma da manyan al'amurran da suka hada da  muhimman tarurrukan a ciki da wajen kasa.

Da kwarewar shuwagabannin ta iya tallata haja ne suka yi nasarar dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari a kasuwannin Najeriya a kusan kowane taron k`asa da k`asa suka halarta. 

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne mataimakin shugaban k`asa Shettima ya bi sahun shugabannin kasashen duniya kimanin 130 a wajen taron BRI karo na 3 da aka yi a kasar Sin, inda ya ja hankalin masu zuba jari daga kasashen waje kan samun saukin harkokin kasuwanci a Najeriya, inda ya bayyana musu cewa, Nijeriyar yau amintacciyar k`asa ce ga masu zuba jari. Daga kasar Sin kai tsaye Shettima ya wuce kasar Amurka don halartar taron tattaunawar k`asa da k`asa na Norman Borlaug don samar da kyautar abinci ta duniya wanda bankin raya kasashen Afirka (AfDB) ya shirya a jihar Iowa, A nan ma mataimakin ya jawo hankulan masu zuba jari tare da shaida musu alkawuran da shugaba Tinubu ya dauka don samar da abinci da habaka tattalin arziki a Najeriya. Daya daga cikin ganimar da VP din ya samo a wannan balugoro ita ce rubanya ayyukan bunk`asa noma na Bankin Raya Afirka (AfDB) a Najeriya inda ya tashi daga dala miliyan 500 zuwa sama da dala biliyan guda.

Bayan watanni biyu da hawansa mulki, mataimakin shugaban k`asa Shettima ya wakilci shugaba Tinubu a wasu manyan tarukan k`asa da k`asa guda har guda biyu a kasashen Roma, Italiya da St. Petersburg inda ya bi sahun sauran shuwagannin duniya a taron farko na (STM) Kazalika ya jagoranci wani babban taro mai taken 'Innovative Financing for Food System Change: the case of Nigeria'.wato taron kirkiro da sabbin dabarun sauya tsarin tallafa wa samar da abinci 

Haka ma a ziyararsa a kasar Rasha don halartar taro tsakanin Rasha da Nahiyar Afirka karo na 2, Shettima ya bi ayarin sauran shugabannin siyasa da 'yan kasuwa a taron tattalin arziki da jin kai na Rasha da Afirka wanda aka mayar da hankali kan dabarun karfafa dangantakar da ke tsakanin Rasha da nahiyar Afirka da dai sauransu. 

VP Shettima ya kuma zauna da manyan jami'an gwamnatin Rasha da shugabannin 'yan kasuwa a kasashen biyu, inda suka tattauna kan huldar dangantakar Rasha da Najeriya.  

Kwanan nan, Sanata Shettima ya tafi birnin Nairobin kasar Kenya, inda ya wakilci shugaba Tinubu a wajen taron shugabannin kasashe masu tasowa(IDA 21).

Wasu daga cikin nasarorinda suka biyo bayan wadannan tafiye-tafiyen sun hada da shawarar da wani kamfanin Amurka, John Deere, ya yanke na zuba jari a fannin noma a Najeriya, inda kamfanin ya ce zai fara da kafa kamfanin hada motocin noma a kasar, sai kuma sabon alkawarin da kasar Sin ta dauka na kammala aikin da aka dade ana dakonsa wato aikin layin dogo daga Legas zuwa Ibadan da Abuja-Kano da Port-Harcourt-Maiduguri. 

Akwai kuma yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu da za ta farauto wa Najeriya sama da dala biliyan 2, zuwa 4. Hakan na nuna irin yawan hannayen jari na kai-tsaye da aka samu a dunkule daga kasashen ketare zuwa ga muhimman bangarori da suka shafi bunk`asa fasaha, motoci da sauran ababen more rayuwa. 

Wadannan yarjejeniyoyin sun hada da kulla kwakkwarar dangantaka tsakanin hukumar  (NASENI) da kamfanonin kasar Sin daban-daban, da kuma alkawurran samar da wutar lantarki da fasahar dijital don tinkarar kalubalen gurbataccen makamashi a Najeriya da bunk`asa sabbin fasahohin zamani masu matukar muhimmanci wajen dorewar ci gaba na  dindindin. . 

A yanzu kasar mu na iya Alfahari da bugun kirji da damammaki masu yawa na bunkasar tattalin arziki da suka hada da hanyoyin inganta samar da wutar lantarki, tsaro, samar da man fetur da iskar gas, sufuri, kamun kifi, yawon bude ido da ma sauran harkokin kasuwanci da zuba jari na k`asa da kasa. Wannan ya nuna k`arara yadda abokan huldar k`asa da k`asa ke k`ara samin kwarin gwiwa kan karfin tattalin arzikin Najeriya daga gwamnatin Shugaba Tinubu da Shattima. 

2. A bangaren NEC

Idan muka komo gida Najeriya ma ba a bar Sanata Shettima a baya ba, domin a matsayinsa na shugaban Hukumar Tattalin Arzikin K`asa ta (NEC), an samar da sabbin shirye-shirye da ayyuka da dama na gwamnatin tarayya a k`ark`ashin ofishin mataimakin shugaban kasar. 

Ga wasu Misalai, NEC ta amince da aiwatar da shirin zuba jari na dala miliyan 617.7 a jihohi 36 da babban birnin tarayya kan fasahar sadarwa ta zamani da k`irk`irarrun hanyoyin saye da sayarwa wato (i-DICE)  domin samar da ayyukan yi a bangaren kere-kere da fasaha ta hanyar horas da matasa sama da miliyan 1.2 kai-tsaye kan fasahar ICT da ma wasu aiyukan da ba na kai-tsaye ba da suka kai milyan 5.6 a fadin kasar. 

A bangaren shawo kan matsalar karancin abinci da na tattalin arziki a k`asa kuwa, hukumar NEC ta yunkura don aikin samar da takin zamani ga manoma, tare da kafa wata runduna da aka yi wa taken Agro-Rangers domin samar da tsaro a gonaki da kuma tabbatar da ana amfani da sabbin dabarun noman zamani. 

Har ila yau, Hukumar ta NEC ce ta jagoranci samar da yankin sarrafa amfanin gona na musamman na gwamnatin tarayya da ake kira (SAPZ) a takaice domin inganta harkar noma a Najeriya tare da rage dogaro da shigo da abinci daga kasashen k`etare.

Majalisar ta NEC k`ark`ashin mataimakin shugaban k`asa ta samar da taswirar yadda za a shawo kan matsalolin ambaliyar ruwa da samar da ingantaccen tsarin bayar da agaji mai samin had`in gwiwar k`ungiyar gwamnoni ta Najeriya.

3. Shirin Pulaku 

Tukuru ofishin mataimakin shugaban k`asa ke aikin sanya ido kan shirin Pulaku, wani sabon tsari na k`ashin kai da gwamnatin Tinubu ta k`irk`iro domin magance musabbabin matsalolin da suka addabi yankunan Arewa wanda suka had`a da rikici tsakanin manoma da makiyaya, da 'yan tada k`ayar baya, da ‘yan fashin daji da tsabar fatara. 

A k`ark`ashin wannan shiri za a gina sama da gidaje 1,000 da asibitoci da shaguna a kowace jaha daga jahohin Arewa maso Yamma domin biyan diyya ga wanda rikicin ya rutsa da su

4. Shirin Haskaka Nijeriya

 A watan Fabrairun wannan shekara, mataimakin shugaban k`asa Shettima ya k`addamar da shirin Light Up South East Initiative, don hanzarta samar da wutar lantarki ga rukunin masana'antu a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, shi dai wannan shiri na had`in gwiwa ne tsakanin Kamfanin Neja Delta Power Holding Company Limited (NDPHC) da abokan huld`ar sa.

A ita dai wannan rana, mataimakin shugaban k`asar ya k`addamar da aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 181 a rukunin masana'antu na Osisioma da ke garin Abar  jihar Abia.

Kazalika Shettima tare da had`in gwiwa da masu ruwa da tsaki da suka himmatu wajen samar da nasarar haskaka Najeriya, ya kaddamar da makamancin wannan  shiri na hasken lantarki a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, shi ma a rukunin masana'antu na Agbara a ranar 12 ga Oktoba, 2023, jihar Ogun, 

5. Shirin Rarraba Ilimi 

A watan Mayun bana ma, mataimakin shugaban k`asar  ya je jihar Bauchi inda ya k`addamar da shiri mai dogon zango na bunk`asa manyan makarantun gaba da sakandare (ASSEP). Daya daga cikin abubuwanda wannan shirin zai gudanar shine gyaran makarantu, da sabunta manhajojin koyarwa, da shigar da fasahohin zamani na gani da ido a fannin koyarwa. 

Wannan shiri wanda zakaran gwajin dafinsa ke Arewa maso Gabas dai wani babban shiri ne na d`inke 6arakar da ilimi ke fama da ita a k`asar nan, 

6. Shirin Sake Tsugunar Da Wadanda Rikici Ya Daidaita

A ranar Litinin din da ta gabata ne mataimakin shugaban k`asa Shettima ya k`addamar da wani shirin kan yadda Jihohi za su samar da hanyar magance matsalolin muhalli ga wad`anda rikici ya raba da garuruwansu 

A wajen k`addamarwar, mataimakin ya yi kira da a had`a hannu da k`asashen duniya don magance matsalar gudun hijira a Najeriya.

Shi dai wannan shiri na daga cikin ajandar Sakatare Janar na majalisar D`inkin Duniya kan samar da mafita ta dindindin ga matsalar matsugunai ga `Yan Gudun Hijira don samar musu da mafita mai É—orewa, da hana sake b`arkewar  rikicin mai haddasa Æ™auracewa muhalli, da kuma tabbatar da waÉ—anda ke fuskantar Æ™aura sun sami ingantaccen kariya da taimako. 

Da yake kaddamar da shirin wanda ake aiwatarwa a jihohi hud`u da suka had`a da Adamawa, Benue, Borno da Yobe, VP ya ce gwamnatin tarayya ta duk`ufa wajen tabbatar da tsaro da jin dad`in ‘yan gudun hijira. 

7. Sake Farfado da Kananan Kasuwanci 

A wani mataki na tallafa wa masu kananan sana’o’i ta hanyar samar musu da dausayin ci gaba, shugaba Tinubu ya fara aikin kafa sana’o’i miliyan d`aya a fad`in Najeriya. A bisa haka ne mataimakin shugaban k`asa Shettima ya k`addamar da dandalin Hab`aka kananan masana'antun MSME na k`asa a garin Makurdi a jihar Benuwe wanda ya zama d`igon d`an-Ba a yunk`urin  k`arfafa wa k`anana da matsakaitan ‘yan kasuwa gwiwa a fadin k`asar nan. Dandalin na MSME, shine irinsa na farko a k`ark`ashin gwamnatin Tinubu, da nufin k`arfafa k`anana da matsakaitan masana'antu (MSMEs) ta hanyar cire duk wani k`alubale da masu masana`antun ke fuskanta da samar musu da damammakin bukatunsu na kasuwanci. Samar da dandalin na MSMEs na da alaÆ™a da kokarin gwamnati na sauke nauyin Alk`awarin da ta d`auka kan sauÆ™aÆ™e hanya ga Æ™ananan 'yan kasuwa. 

Duk da jahar Benue ce ta fara k`addamar da dandalin MSME, ana shirin samar da ire-irensa a duk fadin k`asar inda zai ratsa jihohin Ebonyi, Ogun, Delta, Kaduna, Borno, Katsina da kuma babban birnin tarayya Abuja a kashinsa na farko wanda ya gudana rabin shekarar 2024. 

Kazalika a watan Maris, Sanata Shettima ya k`addamar da kashi na biyu na Shirin fadada kasuwar MSME din ta k`asa a jihar Ogun inda aka mik`a sabbin shaguna har 200 da aka gyara don amfanin ’yan kasuwa 400 a fitacciyar kasuwar Asero Adire da ke Abeokuta. 

8. Magance Talauci Ta  Hanyar Samar Da Kudaden Shiga 

A ci gaba da kokarin da gwamnatin Tinubu ke yi na fitar da ‘yan Najeriya daga k`angin talauci, mataimakin shugaban k`asa Shettima, a ranar 25 ga watan Afrilun bana, ya k`addamar da shirin gwamnatin tarayya na Aso Accord on Economic and Financial Inclusion. Wani shiri mai bangarori da dama da aka tsara domin samun damar shiga tsare-tsaren samun kud`ad`en shiga a fad`in Najeriya. Yarjejeniyar Aso ta samar da ingantaccen tsarin dimokaradiyya don samun damar samun kud`i, k`arfafa wa 'yan kasuwa gwiwa da samar da ci gaban tattalin arziki mai d`orewa tun daga tushe. Shi dai wannan tsari ya zamo tamkar wani yekuwa ne don buÉ—e kowace irin dama ga `yan Najeriya don cimma burin su na tattalin arziki wanda ke wakiltar babbar ajandar sabunta-fata ta gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan mayar da Æ™asar  ga turbar tattalin arziki mai iya tattara  tiriliyan 1 na Dala nan da shekarar 2030 tare da yaÆ™i da talauci da rashin tsaro ta hanyar wadata mai bin doka. 

Ta hanyar amfani da sauye-sauyen da sabbin dabaru a fannonin saka jari, Taswirar Aso Accord ta samar da hanyoyin cike manyan gi6in da ake bari na miliyoyin 'yan Najeriya, musamman mata, matasa, mazauna karkara, da k`ananan 'yan kasuwa, wajen kasa samin muhimman ayyukan samun k`udaden lamuni, inshora, fansho, da wuraren ajiyar kuÉ—i

9. Gina K`asaTa Hanyar Abinci Mai Gina Jiki

A k`ark`ashin k`udirin gwamnatin Tinubu na samar da abinci mai gina jiki da rahusa, kwanan nan mataimakin shugaban k`asa Shettima ya k`addamar da wani gagarumin shiri na inganta abinci mai gina jiki a fadin Najeriya, tare da yin kira ga Shugabannin addini da na gargajiya da su jagoranci wannan yunkuri a yankunansu. 

A wajen babban taron tattaunawa kan abinci mai gina jiki da aka gudanar a fadar shugaban k`asa,, VP Shettima ya jaddada cewa ba kawai a kan wadatar abinci ci gaban Najeriya ya ta’allaka ba,, har ma da samar da abinci mai gina jiki. Tattaunawar ta yini d`aya mai taken, “Jagororin Addini A  Matsayin Masu Kayatar da Jikin Dan Adam Ta Hanyar Gina Jiki,” Majalisar Kula da Gina Jiki ta K`asa da Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya da ke Tallafa wa [ANRiN] Project ne suka shirya taron.

A k`ok`arin Kwamitin NEC k`ark`ashin jagorancin mataimakin shugaban k`asa da had`in gwiwar shuwagabannin addinai da ma wasu masu ruwa da tsaki, an dauki aniyar samar da fasalin dak`ile yunwa da rashin abinci mai gina jiki da k`alubalen da ke tattare da su. 

10. Ba Sani Ba Sabo Kan Noma 

Bisa la'akari da 6arnar da aka tafka a wasu muhimman bangarori da suka had`a da noma na tsayin shekaru. Da hawa karagar mulkin Shugaba Tinubu, a shekarar da ta gabata, ya fara aiwatar da sauye-sauye masu tsauri don kawo gyara a fannin noma. Roko na farko da shugaban  ya yi shi ne ‘yan Najeriya su koma gona, domin da ruwan ciki ake Jan na rijiya.

Shugaba Tinubu bai yi k`asa a gwiwa ba wajen kafa dokar ta-baci kan samar da abinci. A wani 6angare na k`ok`arin da sabuwar gwamnatin ta yi na shawo kan hauhawar farashin kayan abinci bayan radadin da cire tallafin man fetur ya haifar shugaban ya kuma amince da shigar da duk wani abu da ya shafi sauk`ak`a samar da abinci da ruwa cikin rukunin farko na ababen more rayuwa, kuma ya sanya su cikin  aiyukan Majalisar Tsaron Kasa.

A fannin farfado da fannin bunk`asayawan amfanin gona a gida da bunk`asa tattalin arzikin kasar kuwa, shugaban ya bayyana wasu tsare-tsare da suka hada da fad`ad`a filayen noma zuwa hekta 500,000, da samar da rancen kud`ad`e masu k`arancin ruwa ga manoma da zuba jari a fannin noman rani. Hakan ya biyo bayan sakin takin zamani da iri ga manoma da magidanta don rage radadin cire tallafin.  

A watan Maris d`in bana ne ‘yan Najeriya suka fahimci dimbin amfanin da ke tattare da jarin da Tinubu ya zuba a bangaren noma a yayinda shugaban ya k`addamar da shirin samar da abinci da sarrafa kayan gona a Minna, babban birnin jihar Neja. Aikin wani shiri ne na gwamnatin jihar Neja mai niyyar amfani da manyan injinan noma da fasaha domin bunk`asa amfanin gona a jihar. 

A karon farko k`ark`ashin gwamnatin Tinubu, Najeriya ta fara shaida wani sabon salo na  aiki tare tsakanin shugaban k`asa da mataimakinsa. Misali, yayin da Shugaba Tinubu ke zaburar da gwamnatocin k`asa baki daya wajen ganin sun shiga cikin tsarin hab`aka noma na gwamnatin tarayya, a kullun za ka ji VP Shettima na tabbatar da cewa  gwamnatinsu na da fatan zama a bar koyi.

 A Shekarar bana, mataimakin shugaban kasar ya fitar da nasa tsarin k`arfafa wa manoman kasar nan don cimma nasarar shirin samar da abinci da aikin noma na gwamnatin Tinubu. Shirin mai suna Kashim-Shettima Foundation's Agricultural Empowerment Programme, wanda aka k`addamar a jihar Kaduna, ya nuna cewa an fara rabon taraktoci, da iri, da takin zamani, da magungunan kashe kwari, da sauran muhimman kayan noma ga manoman da za su amfana da noman shekarar 2024.

Bugu da kari, shirin ya kuma ba da damar samin tallafin k`arfafa gwiwa ta hanyar bayar da N100,000 ga kowane daya daga cikin masu cin gajiyar shirin guda 50 a tsawon watanni 4 na lokutan shuka.

 Hakazalika za a bai wa kungiyoyin manoman da suka kunshi manoma 50 kud`ad`en fara aiki har Naira miliyan 30 domin kafa gonakin kasuwanci.

Salon shugabancin da Kashim Shettima ke son bari a matsayinsa na lamba biyu a Najeriya shi ne koyar da bautar k`asa da sadaukar da kai, rikon amana, biyayya ga gwamnatin Tinubu. 

A ko ina ka hadu da Kashim bashi da aiki sama da ya nuna nagartar maigidansa, wadannan halayen nasa da ma wasu na salon shugabancinsa sun sa ‘yan Najeriya da dama na kaunarsa da  ganinsa a matsayin cikakken mataimaki ga shugaban kasa. 

Lallai idan aka ce a ci gaba da ninkaya a bayani kan nagarta da hankalin Kashim, Alkaluma  da yawa za su bushe ba tare da an kammala ba.

 HaÉ—in kai da amincin da ake gani tsakanin shugabannin biyu na da ban sha'awa, domin duka mutanen biyu a cikin shekara d`aya da kama mulkinsu sun nuna kamanceceniya wajen hidimta wa kasa da sadaukarwa da kuma gaskiya a cikin shugabanci.  Kuma Mataimakin shugaban k`asar yayi nasarar cusa ak`idar biyayya ga shugaban k`asa a zukatan duk wanda ke aiki tare da shi don samar da hadin kai, aiki tare don inganta Najeriya. 

A dunk`ule za mu iya cewa idan aka yi la`akari da irin matakan da gwamnatin shugaba Tinubu ta d`auka, ko shakka babu Najeriya na gab da shiga k`ungiyar k`asashen da suka ci gaba. 


Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musamman

ga shugaban k`asa kan harkokin yada labarai da sadarwa, 

(Ofishin mataimakin shugaban kasa)


No comments