Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nijeriya Ta Buƙaci A Daina Ruwan Wuta A Gaza Nan Take

Nijeriya ta yi Allah wadai da kisan fararen hula a Gaza, ta kuma yi kiran a gaggauta wanzar da zaman lafiya a yankin. Wata sanarwa da minist...



Nijeriya ta yi Allah wadai da kisan fararen hula a Gaza, ta kuma yi kiran a gaggauta wanzar da zaman lafiya a yankin.

Wata sanarwa da ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya fitar ta ce gwamnatin ƙasar ta damu da halin da fararen hula suka shiga yanzu haka a Gaza, saboda harin da Isra'ila ke kai wa kan Falasdinu.

Harin baya-bayan nan da Isra'ila ta kai kudancin Gaza a ranar Lahadi 26 ga watan Mayu ya kashe mutum aƙalla 45, mafi yawan su mata da ƙananan yara, lamarin da ya ƙara yawan hare-haren da aka kai kan fararen hula tun bayan ɓarkewar yaƙin.

Sanarwar gwamnatin Nijeriyar ta koka da yadda aka riƙa samun rashin mutumta yarjejeniyar tsagaita wuta da cin zarafin ɗan'adam da kuma hana shigar da kayan tallafi Gaza daga Isra'ila.

Nijeriya ta buƙaci a gaggauta komawa tsarin kiyaye ƴancin ɗan'adam, musamman hana kisan gilla da kuma kare fararen hula da ke Gaza daga duk wani harin soji.

Ta kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, da suka haɗa da Isra'ila da Hamas da kuma Majalisar Dinkin Duniya su ƙara mayar da hankali kawo ƙarshen rikicin Gaza domin tsagaita wuta da kuma ceton fararen hula a yankin.

No comments