Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Kano Ya Gana Da Nuhu Ribadu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gana da babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu a Abuja. ...



Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gana da babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu a Abuja.

Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ya ce ya yi muhimmiyar ganawa da Nuhu Ribadun.

Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce gwamnan ya gana da Nuhu Ribadun ne kan abin da ke faruwa a Kano na rikicin masarautu.

Dawakin Tofa ya ƙara da cewa mutanen biyu sun kuma tattauna wasu batutuwan da suka jiɓanci zaman lafiya da ci gaban ƙasa a lokacin ganawar tasu.

A ƙarshen makon da ya gabata ne mataimakin gwamnan Kano, Comr. Aminu Abdulsalam ya zargi Nuhu Ribadun da kitsa komawar sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero zuwa birnin, kwana biyu bayan da gwamnan jihar ya sanar da tuɓe shi daga sarauta.

Sai dai ofishin Ribadun ya musanta zargin tare da barazanar maka mataimakin gwamnan a kotu idan bai janye kalaman nasa ba.

Daga bisani dai mataimakin gwamnan ya janye kalaman nasa tare da bai wa Ribadu haƙuri, yana mai cewa da farko ba su fahimci yadda batun yake ba.

No comments