Daga Awwal Umar Kontagora Shugaban jam'iyyar APC a jihad Neja, Hon. Aminu Musa Bobi ya bayyana cewar gwamnatin manomi Rt. Hon. Uma...
Daga Awwal Umar Kontagora
Shugaban jam'iyyar APC a jihad Neja, Hon. Aminu Musa Bobi ya
bayyana cewar gwamnatin manomi Rt. Hon. Umar Mohammed Bago ta samarwa jihar
Neja martaba da tagomashin da ba wata gwamnatin da ta samar da irinsa tun bayan
kafuwar jihar. Shugaban ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da gwamnatin ke
cika shekara daya kan madafun ikon jihar.
Bobi, ya cigaba da cewar bayan zuwan Bago kan karagar mulkin
jihar wanda uba ne kuma cikakken dan jam'iyyar APC ya kafa dambar gina hanyoyi
guda dari biyar da ashirin da shi a fadin jihar, wanda manyan kananan hukumomin
jihar kamar Suleja, Kontagora da Bida dukkansu zasu samu kaso na aikin hanya
kimanin kilo mita talatin da biyar zuwa arba'in da biyar yayin da sauran
kananan hukumomi zasu ci ribar kilomita biyar zuwa sama, wanda a halin yanzu ba
karamar hukumar da ba a fara aikin ba.
Idan ka dawo shalkwatan jiha, wato Minna za a gina hanyoyi
kilomita dari da doriya, wanda tun daga karamar hukumar Paikoro zuwa cikin
garin ko wanda bai san fadar gwamnatin jiha zai shaidi cewar an samu gwamnati
mai kishin cigaban jihar nan.
Wannan ne ya janyowa jihar Neja, kambin yabo da girmamawa
idan ka kwatanta da jahohin yankin arewa ta tsakiya, wanda sauran gwamnoni da
shugabannin jam'iyya sun yaba da irin yunkurin Mohammed Bago na martaba jam'iyyar
nan a wannan yankin.
Bayan zuwan Umar Bago, ya bada political appointment sama da
dubu takwas ga yayan jam'iyya, wanda dan abinda ake amsa na hakkin jam'iyya
daga albashin masu mukaman siyasa daga tarayya har zuwa kananan hukumomi, shi
muke tattarawa muka biya bashin kudin haya na kusan shekaru hudu da ake bin mu,
bayan nan mun baiwa yayan jam'iyya sama da dubu bakwai appointment wanda mai
karamin albashi na karban naira dubu arba'in.
Bisa kwarin guiwar da wannan gwamnatin, yasa muka himmantu
wajen kafa wani abu na tarihi da zai karawa jam'iyya samun gindin zama da
karbuwa na samar da sakatariyar jam'iyya mai zaman kan ta, wanda a tarihin
Afrika ba za a samu irinsa, wanda muke sa ran kashe sama da naira biliyan biyu
a ginin sakatariyar jiha kawai.
Saboda haka, kudurin mu shi ne duba da kyakkyawar manufa da
burin da gwamna Bago yake da shi a jihar nan, da sauyin da ya kawowa siyasar
jihar nan, dukkanin wadanda suka samu appointment daga matakin tarayya zuwa
kananan hukumomi har wanda jam'iyya ta bayar mutane ne da idan lokacin zabe
yazo 2027 zasu iya kawo kuri'un wasu wanda abinda zamu nema ciko ne dan gwamna
Bago ya cigaba da jan ragamar jihar nan.
Abinda muke kuduri idan Allah ya ba mu aron rayuwa, kamar
yadda gwamna ya aza tubalin ginin jihar nan, a bangaren hanyoyi, kiwon lafiya,
da dawo da martabar noma da kiwo, shi ne goya masa baya a 2027 dan cigaba da
wadannan ayyukan na alkhairi a jihar Neja.
Da yardar Allah, muna tsare tsaren da jam'iyya da kan ta za
ta sayawa gwamna fom dan samun zagon na biyu ba tare da hamayya ba, wanda duk
wani zababbe da ya taka rawar gani wajen kawo cigaba a jihar nan da jam'iyyar
APC za mu tabbatar jam'iyya ce ta zama gata gare shi dan cigaba da ayyukan
alheri na ayyukan raya kasa a jihar nan.
Hon. Aminu Bobi, ya jawo hankalin yayan jam'iyyar APC da su
kara azama wajen gina jiha da jam'iyya, su watsar da batutuwan yan adawa domin
adawarsu ba zai hana gwamnati cigaba da ayyukan da ta sanya a gaba ba, fatar
wannan gwamnatin bisa jagoranci uba kuma cikakken dan jam'iyya shi ne samar da
sabuwar jihar Neja.
Matasa sun rungumi hanyoyin dogaro da kai, gwamnati za ta
samu kwarin guiwa wajen kawo ayyukan alheri da samar da abubuwan more rayuwa da
aka yi mana tazara ne muddin matasa suka zama masu kishin kan su da kasa ne,
wanda akwai zaratan yan siyasa masu kawo shawarwari nagartattu da gwamnatin
jiha ke anfana da su wajen gina jiha.
No comments