Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar Makafi Ta Karrama Janar Abdussalam Da Lambar Yabo

Daga Awwal Umar Kontagora Ƙungiyar makafi ta Nijeriya, wato Nigeria Association of Blind, reshen jihar Neja ta karrama tsohon sh...

Daga Awwal Umar Kontagora

Ƙungiyar makafi ta Nijeriya, wato Nigeria Association of Blind, reshen jihar Neja ta karrama tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdussalam da lambar yabo. Tunda farko a bayaninsa, kakakin kungiyar ta kasa, Comr. Abdurrahaman Awwal Bida, ya bayyana cewar matakin karramawar ya biyo bayan goyon baya da tallafin da yayan kungiyar ke samu da kwarin guiwa daga tsohon shugaban ƙasar.

Yace uwar kungiyar ta nemi alfarmar tsohon janar din ya zama ga kungiyar a jihar Neja ta yadda zasu kara samun isar da bukatun yayan kungiyar domin samun tallafin da yake ba su da isar da bukatunsu ga gwamnatin da kuma samun kulawar da ta dace.

A bayanin shugaban kungiyar ta jihar Neja, Malam Hamza Salihu, ya bayyana cewar yanzu haka kusan cibiyoyin horar da makafi a fâdin jihar nan sun mutu, kuma yara masu tasowa da Allah ya jarabce su da lalurar rashin gani akwai sama da ashirin da suka kammala karatun NCE amma ba ayyukan yi.

"Muna da wata cibiyar horar da makafi a karamar hukumar Bida, kusan na'urar da ake anfani da shi wajen kpyarwa ta tsaya, sannan a karamar hukumar Suleja, muna bukatar gidan makafi mallakin gwamnati, yanzu haka da daman mu suna da iyalai, amma ba su da mafita.

Maigirma tsohon shugaban kasa, muna neman alfarma da a saurari bukatun mu muna da jama'a da dama da suke da kwarewa kuma masu ilimi amma kusan anfani ga gwamnati ko yan siyasa sai lokacin zabe kawai, amma da zaran an kammala an kai ga madafun iko sai a watsar da mu.

A bayaninsa, tsohon shugaban kasar, Janar Abdussalam Abubakar yayi kira ga masu hannu da shuni da yan siyasa da su rika taimakawa musamman a bangaren ilmi musamman ga yayan masu bukata ta musamman.

Janar ya yabawa karramawar kuma yayi alkawalin a matsayin shi na uban kungiyar zai tabbatar ya taka rawar gani wajen inganta rayuwar makafi da yayan su a jihar Neja.

Ya ce duk da cewar akwai ma'aikatar jinkai da tallafawa jama'a a jiha, zai shawarci gwamnati wajen ganin an samar da hanyoyin inganta rayuwar masu bukata ta musamman.

Daga cikin wadanda aka karrama akwai tsohon shugaban kasa, Janar Abdussalam Abubakar, da jami'i mai kula da harkokin nakassasu kuma kakakin ƙungiyar ta ƙasa, Comr. Abdurrahman Awwal.

No comments