Daga Awwal Umar Kontagora Kwamishinan ma'aikatar manoma da makiyaya ta jihar Neja, Hon. Ahmad Umar Sanda ne ya bayyana cewa ...
Daga Awwal Umar Kontagora
Kwamishinan ma'aikatar manoma da makiyaya ta jihar Neja, Hon. Ahmad Umar Sanda ne ya bayyana cewa a yunƙurin gwamnatin jiha na jin daɗi da inganta rayuwar makiyaya kashi talatin cikin ɗari na makarantun da suka durƙushe gwamnati ta farfaɗo da su.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ɗaurin auren yar Ardo Tukur Abubakar wani Basaraken da ya kafa makarantar makiyaya mafi tarihi da ta yaye ƴaƴan Fulani da dama.
Ya ce ilmantar da 'ya'yan makiyaya ilimin zamani da na addini, bayan samar masu abubuwan more rayuwa kamar tsaftaccen ruwan sha da za su yi anfani da shi kuma su shayar da dabbobinsu, ilimantar da su shi damba na biyu da gwamnatin jiha ta sanya a gaba.
Akwai makarantun da ke da matsalar malamai saboda nisan guri, yanzu gwamna ya bada umurni mu samar da karin malamai wadanda ke kusa da matsugganan makiyaya, kuma yanzu haka hukumar UBE na cigaba da daukar malamai.
Bayan nan akwai makarantun da kwata kwata sun daina wanzuwa kuma akwai al'ummomi da dama da ke zama wuraren, maigirma gwamna ya bada umurnin mu sake bude kuma tabbatar iyayen yara sun dawo da yayan su dan cigaba da karatun.
Yanzu haka dukkanin shiyyoyin nan uku na Neja, ba bangaren da ma'aikatar mu ba ta taba ba, saboda dukkanin bangarorin kananan hukumomi ashirin da biyar suna da wakilci a ma'aikatar mu.
Dukkanin matsalolin makiyaya da manoma mun san su, kuma gwamnan jiha, Rt. Hon. Umar Mohammed Bago na ba mu goyon baya dan cin ma kudurin gwamnatinsa na farfado da ilimin yayan makiyaya da manoma dan yin gogayya da zamani.
Ardo Tukur Abubakar, mai bai wa gwamna shawara akan harkokin makiyaya, ya ce mu al'ummar Fulani maigirma gwamna ya nuna mana da gaske yake, yanzu kafin zuwan gwamnatin makarantar nan mun assasata shekaru da dama, akwai yaran mu da suka kammala karatunsu a nan, wasu yanzu haka suna makarantun gaba da sakandare, wasu sun kammala ma.
Amma bayan zuwan gwamna Bago bayan karin malamai da aka samun, ga makarantar har da wutan lantarki an sanya mata. Kuma a kullun kwamishinan mu a tsaye yake wajen sauraren matsalolin makiyaya da manoma tare da daukar matakan da suka dace.
Ardo Tukur, ya jawo hankalin iyaye musamman wadanda ke zaune a cikin karkaru da su tabbatar wannan garabasar da gwamnatin Neja ta yiwa yayan makiyaya da manoma ba abar su baya ba.
No comments