Daga Hussaini Yero, Funtua Gwamnan Jihar Zamfara,Dauda Lawal ya tabbatar da ya gaji Bashin sama da Naira Biliyan Sha uku na tsa...
Daga Hussaini Yero, Funtua
Gwamnan Jihar Zamfara,Dauda Lawal ya tabbatar da ya gaji Bashin sama da Naira Biliyan Sha uku na tsafin Ma'aikata da suka aje aiki watau Giratuti da Fensho.daga gwamnatocin da suka gabata.
Dauda Lawal ya bayyana haka ne a wajan taron bikin cika shekara daya da hawansan mulkin Zamfara yau a Gusau babban birnin Jihar Zamfara.
"Acewar sa ,Bashin da na gada ne daga gwamnatocin baya daga shekara ta 2012 zuwa 2023. A yanzu haka na biya Naira Biliyan biyar ga Tsafin ma'aikatan kuma ya da yarda Allah duk wata zan rinka biya har na kammala.inji gwamna Dauda.
Haka kazalikama kuma gwamna Dauda Lawal ya bayyana nasara da ya samu na karuwar kudin shiga wanda a shekara guda da yayi Jihar Zamfara ya tara naira Biyan biyu a shekara guda.sabanin naira Miliyan dari da a ke samu daga gwamnatin da ta Fadi."
" Dan haka da yardar Allah da wadannan kudaden ne zamu cigaba da yima alumma ayyukan cigaba da muka dauki alkawari a lokacin yakin cin Zabe.
No comments