Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Neja Za Ta Kai 'Ya'yan Fulani Kasashen Turai Domin Samun Ilimin Zamani

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnatin Neja ta kuduri aniyar kai yayan Fulani makiyaya kasashen turai dan samun ilmin zamani. Gwamnan Neja,  Ma...



Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnatin Neja ta kuduri aniyar kai yayan Fulani makiyaya kasashen turai dan samun ilmin zamani. Gwamnan Neja,  Manomi Umar Mohammed Bago ne ya bada tabbacin hakan a lokacin bude sakatariyar kungiyar Bago Ruga-Ruga a karkashin jagorancin Alhaji Hassan Shiroro ( Wakilin fulanin Minna, Garkuwan Woro Maliki).

Bago, ya cigaba da cewar Fulani ba yan ta'adda ba ne, domin shi asalin jinsin Fulani ne kuma yana da tabbacin Fulani mutane ne masu amana, kaifin hankali da ilimi da hangen nesa. A kokarin gwamnatin sa na inganta ilmin yasa ya umurci ma'aikatar kula da harkokin makiyaya da manoma da ta tabbatar dukkan makarantun nomadic a jihar nan an farfado da su dan ganin yayan Fulani ba a bar su baya ba.

Gwamnan ya bada tallafin naira miliyan ashirin dan rabawa matan makiyaya dan samun damar cigaba da kananan sana'o'i da kiwo dan samun dogaro da kafarsu.

Tunda farko dai, a taron kamfanin Morris Fertilizer Limited, ya bada tallafin naira dubu hamsin ga mata hurhudu daga dukkanin yankunan kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar.

A bayaninsa, shugaban kungiyar Bago Ruga-Ruga, Alhaji Hassan Shiroro, yace sun bude wannan sakatariyar ne dan kara jadadda goyon bayan su ga manufofin manomin gwamna Umar Mohammed Bago, domin ya nanuwa Fulani makiyaya karamci a lokacin yakin neman zabe, kuma dukkanin alkawurran da ya yiwa al'ummar Fulani ya cika su.

Alhaji Hussaini Yusuf Bosso ( Ardon Fulanin Paiko) kuma tsohon shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breaders ta kasa, ya jawo hankalin iyaye da shugabanni da su tashi tsaye wajen wayar da kan matasa muhimmancin neman ilimi da zaman lafiya, domin babu al'ummar da za ta cigaba muddin ba ta da ilimi kuma babu zaman lafiya tsakanin su da abokan zama.

Ardon, ya bayyana cewar tun bayan dawowar tsarin dimukuradiyya ba dan siyasar da ya janyo al'ummar Fulani a jika ya nuna suna da muhimmancin kamar Rt. Hon. Umar Mohammed Bago.

Dan haka muna umurtar matasa maza da mata kowa ya tabbatar ya mallaki katin zabe domin ba wani dan siyasar da za mu kara marawa baya, sai mun san kudurinsa akan al'ummar Fulani. Domin dan uwan mu gwamna Umar Mohammed Bago ya wayar muna da kai, ya kuma nuna mana muhimmancin gwamnati da alfanun tafiya tare.

Tsohon jagoran na kasa, ya jawo hankalin Fulani muhimmancin neman na kai, dogaro da kafa da kuma kaucewa yawon roko, maula da illar barace barace ga dan Adam. Mu sani muna wakiltar harshen fulatancin ne ya zama wajibi a duk inda muka samu kan mu lallai mu kare martabar harshen nan.

Malam Abubakar Agaji Mariga, wani matashi ya yabawa jagororin Fulani da su ka tsaya kai da fata wajen ganin an tafi al'ummar Fulani a gwamnatance, wanda kowa shaida ne mu dai Fulani makiyaya mun yaba kuma muna godiya ga manomi gwamna Umar Bago kan wannan sauyin rayuwa da ya samarwa al'ummar Fulani a jihar Neja.

Hon. Ahmad Umar Sanda Rabe, kwamishinan ma'aikatar kula da harkokin makiyaya da manoma, yace zuwa kashi tamanin cikin dari na matsalolin makiyaya da manoma sun kau tun bayan kirkiro wannan ma'aikatar.

Yanzu haka akwai matsalar tallace tallace ga yaya mata, muna kokarin kammala shirye shirye da wasu kamfanoni da zasu rika shiga rugage dan kulla cinikin madara da makiyaya ba sai mata sun rika titi da cikin gari suna talla ba.

A yankin Neja ta tsakiya kawai muna sa ran fitar da madara lita dubu dari takwas a kowace rana, ke nan idan duka shiyyoyi uku na jihar aikin ya kan kama za mu iya fitar dubban litocin madara, ka ga ke nan maganar tallar nono akan hanyoyi ya kare.

Kwamishinan ya nemi Fulani makiyaya da su cigaba da baiwa gwamnati goyon baya, akwai shirye shirye da dama da gwamnati ta kudurta da zai anfanar a jihar nan ga makiyaya da manoma.

No comments