Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar Hafizan Alkur'ani da Malamai ta Nijeriya wacce aka fi sani da 'Huffazul Qur'an and Islamic Sc...
Daga Awwal Umar Kontagora
Kungiyar Hafizan Alkur'ani da Malamai ta Nijeriya wacce aka fi sani da 'Huffazul Qur'an and Islamic Scholars Association of Nigeria' karkashin jagorancin Gwani Hussaini Abubakar Shakwata ta mika ta'aziyyarta ga 'yan'uwa da abokan arziki musamman tsohon gwamnan Neja, Dakta Mu'azu Babangida Aliyu (Talban Minna) bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Jamila Aliyu ( Ya Jami).
Hajiya Jami ta rasu a yammacin Litinin din makon nan, za a yi jana'izarta a yau Talata da misalin karfe biyu na rana a harabar babban masallacin juma'a da ke cikin garin Minna.
Kungiyar ta bayyana rashin wannan dattijuwar rashi ne babba da ya shafi al'umma da dama sakamakon gudunmawa da taimakon da ta ke yiwa mabukata.
A wani bangaren kuma, shugaban kungiyar reshen arewa ta tsakiya, Ambasada Gwani Musa Adamu yace Hajiya Jami uwa ce da ba za a iya mantawa da alheranta ba
Dan haka kungiyar tayi addu'ar samun rahama gare ta bisa ayyukan ta na alheri da ta aiwatar a lokacin rayuwarta.
No comments