Daga Fatima Idris Rundunar Æ´ansandan Najeriya reshen jihar Legas ta cafke mutum sama da 50 bayan hargitsin da ya kaure tsakanin wasu matasa ...
Daga Fatima Idris
Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Legas ta cafke mutum sama da 50 bayan hargitsin da ya kaure tsakanin wasu matasa da ɓatagari a yankin Ile-Epo da ke jihar Legas.
A sanarwar da kakaknin rundunar, SP Benjamin Hundeyin ya fitar ranar Alhamis, babban jami’in É—ansanda yankin ya tura jami’ansa zuwa wajen inda kuma tuni aka maido da zaman lafiya.
Sanarwar ta ce an lalata rumfunan da suke zaune.
Kwamihsinan Æ´ansanda CP Adegoke Fayoade ya bayar da umarnin a gurfanar da mutanen da aka kama inda kuma ya yi gargaÉ—i cewa rundunar za ta É—auki mataki kan duk wanda aka samu da ta da zaune tsaye.
Wakiliyarmu ta zanta da shugaban kungiyar masu ciret na ƙasa kuma sakataren kungiyar masu sayar da abinci na ƙasa Malam Ahmad Alaramma akan yadda lamari ya faru.
Ya ce matsala ce ta tashi a kasuwar tsakanin wani matashin Bahaushe da wani matashin Bayarabe akan kuɗi dan ƙankani.
Shugaban ya ce akan kuɗi 'yan ƙalilan ne lamarin ya taso amma sai abin ya koma faɗan ƙabilanci wanda a yanzu an jima mutane da dama rauni kuma an ƙona mana Kiret na a ƙalla kudi Naira Miliyan Dari Uku da Sittin wanda ba za mu amince da faruwan irin wannan ɓarna ba.
Ƙarshe shugaban ya yi barazanar dakatar da kai Tumatur jihar Legas (Ele epe)
Kuma ya yi kira ga gwamnati cewa irin taimakon da kungiyar ta su ke bayarwa bai kamata a ce ana yin mata cin zarafi irin haka ba.
Ya tabbatar da cewa a ƙalla kungiyar tana da mutane sama da mutum dubai wanda suke ciyar da iyalansu abinci karkashinta wanda haka ya nuna cewa kungiyar tana da muhimmanci kuma ta ragewa gwamnati wani aiki.
Kuma yayi fatan gwamnati zata sa bak byi a cikin lamarin.
Bincike na nuna cewa zuwa yanzu hukuma ta shigo cikin lamarin amma bata ce komiaba.
No comments