Hukumar kula da harkokin lantarki ta Najeriya ta ce ta tura wa gwamnatin tarayya buƙatar shiga tsakani kan yadda wasu ƴan ƙasashen waje ba...
Hukumar kula da harkokin lantarki ta Najeriya ta ce ta tura wa gwamnatin tarayya buƙatar shiga tsakani kan yadda wasu ƴan ƙasashen waje ba su son biyan bashin da ake bin su na kuɗin wuta.
Hakan na ƙunshe cikin rahoton zango na huɗu na 2023 da hukumar ta wallafa a shafinta.
Rahoton hukumar ya ce a cikin wannan lokacin kamfanonin raba wutar lantarki da wasu kamfanonin ƙasashen waje huɗu ba su biya kuɗin wutar da suka sha har jimillar naira biliyan 97.5.
Ƙididdigar da aka wallafa ta nuna cewa ana bin kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 kuɗi naira biliyan 81, yayin da kuma ake bin kamfanonin ƙasashen wajen naira biliyan 16.5 a zangon ƙarshe na 2023.
No comments