Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ana Ƙoƙarin Zaƙulo Mutane 30 Da Ƙasa Ta Rufta Da Su A Neja

Mutum 30 ne ƙasa ta danne bayan wani ramin haƙar ma'adanai ya rufta a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya. Hukumar bayar da agajin gaggaw...



Mutum 30 ne ƙasa ta danne bayan wani ramin haƙar ma'adanai ya rufta a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja ta tabbatar da cewa mutum ɗaya ya mutu yayin da aka ceto mutum shida waɗanda suka samu raunuka.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Galkogo da ke ƙaramar hukumar Shiroro, kuma ana ganin cewa mamakon ruwan sama da aka samu ne ya haifar da lamarin.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar ta Neja, Abdullahi Baba Arah ya tabbatar wa BBC a safiyar yau Laraba cewa ana wani yunƙuri na samar da iskar shaƙa ga mutanen da ke maƙale a ƙarƙashin ƙasa.

Neja na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya waɗanda ke ƙunshe da albarkatun ƙasa masu yawa, wadda kuma ke fama da matsalar tsaro.

A irin waɗannan yankuna akan samu wuraren haƙar ma'adanai da ke aiki ba bisa ƙa'ida ba kuma ba a ɗaukan matakan kariya da suka kamata.


No comments