Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kashi 70 Cikin Ɗari Na Yara A Nijeriya Ba Su Iya Karatu Da Lissafi Ba

Hukumar tsara harkokin ilimi da gudanarwa ta Najeriya (NIEPA-NIGERIA), ta nuna damuwarta kan yadda Kashi 70 cikin ɗari na yara a Najeriya ba...



Hukumar tsara harkokin ilimi da gudanarwa ta Najeriya (NIEPA-NIGERIA), ta nuna damuwarta kan yadda Kashi 70 cikin ɗari na yara a Najeriya ba sa iya karatu da lissafi mai sauƙi, kamar yadda wani rahoto ya nuna.

Bayanin wani ɓangare ne na binciken da aka yi kan nasara ko cigaban koyo a Najeriya, wanda ya fito da irin matsalolin da tsarin ilimi yake da su a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban hukumar, Dr David Shofoyeke, shi ne ya nuna damuwar a lokacin yayin buɗe wani taron kara-wa-juna-sani na malamai da manyan jami'an kula da ilimi da shugabannin makarantu, na jihohin arewa maso yamma, kan tafiyar da harkokin makarantu a ƙarni na 21.

Shugaban ya kuma lura cewa kashi 49 cikin ɗari ne kawai na yara da ke zuwa makaranta suke iya karatu da kuma fahimtar abin da suka karanta.

A ɓangaren lissafi kuma ya ce, kashi 55 cikin ɗari ne kawai ke iya lissafi mai sauƙi.

No comments