Mun samu Labarin rasuwar Ciritawan Zazzau Alhaji Isyaku Muhammad Ashiru mai shekaru 92 bayan ya yi fama da doguwar jinya. A wata...
Mun samu Labarin rasuwar Ciritawan Zazzau Alhaji Isyaku Muhammad Ashiru mai shekaru 92 bayan ya yi fama da doguwar jinya.
A wata sanarwa da ta samu sanya hannun Wakilin YaÉ—a labaran Masarautar Kudan Yusuf Ibrahim kudan.
Alhaji Isyaku Muhammad Ashiru kafin rasuwarsa ya taɓa zama Hakimin Kudan a yankin ƙaramar hukumar Kudan a jihar Kaduna.
Marigayin ya rasu ya bar mata 3 da 'ya'ya 24 da jikoki da dama da kuma Æ´an uwa maza da mata.
Cikin su akwai Mayanan Arewan Zazzau kuma Hakimin Hunkuyi Aminu Muhammad Ashiru, sai Alhaji Isa Muhammad Ashiru Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a zaɓen Shekara ta 2023 da wasu da dama.
An yi jana'izarsa da misalin 5 na yammacin ranar Lahadi A fadar garin Kudan.
No comments