Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gudunmawar Sanata Barau Wajen Magance Matsalolin Arewa Maso Yammacin Nijeriya

Daga Aliyu Samba Daga cikin muhimman ƙudurai da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin Maliya y...

Daga Aliyu Samba

Daga cikin muhimman Æ™udurai da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin Maliya ya É—auki nauyin kawowa gaban Majalisa, akwai Æ™udurin samar da Hukumar BunÆ™asa Arewa maso yammacin Najeriya (NWDC). Manufar wannan Æ™udurin shine samar da tallafi na musamman da zai magance matsalolin da suke addabar wannan yankin. 

Kamar yadda yake sanannen abu wajen É—an Najeriya, yankin Arewa maso yamma na fuskantar matsaloli da suka haifu sakamakon ayyukan ta'addanci da yan bindigar daji, mahara, É“arayin daji, Æ´an fashi da makami, masu garkuwa da mutane da yan Boko Haram suka haifar, wanda suka jawo koma baya a fannoni daban-daban na cigaban yankin. 

Sanata Barau yayin gabatar da wannan Æ™udurin na kafa Hukumar ta BunÆ™asa Arewa maso yammacin Najeriya, ya bayyana cewa; 

''Arewa Maso Yamma a matsayin sa na yanki ya bada gudummawa sosai wajen ci-gaban Najeriya musamman a fannin noma da sauran abubuwan da suka shafi cigaban Æ™asar nan, amma har yanzu yankin na fama  da mummunan koma baya''

''Abinda yankin yake buÆ™ata a yanzu shine Gwamatin Tarayya ta tallafa wajen samar da hanyoyi da kayayyakin inganta rayuwa da ilimantar da É—imbin matasan yankin tare da samar da hanyoyin bunÆ™asa yankin gaba É—aya ta yadda zai bunÆ™asa kamar ko fiye da sauran shiyyoyin kasar nan''. 

''Ta'asar yan ta'addan bindiga da masu garkuwa da mutane sun yi matuƙar lalata ababen inganta rayuwa a sassan yankin, lamarin daya jawo ficewar masu zuba hannun jari da yan kasuwa da masu gudanar da kamfanoni da ma'aikata daga yankin. Wannan ya jawo muguwar illa ga harkokin tattalin arzikin yankin, tare da ƙarancin abinci da rashin aikin yi, wanda a baya yankin yayi ƙaurin suna wajen noma da siyar da kayan abinci a yankin Sahel''

''Don haka, wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali wajen magance waÉ—annan matsaloli da Æ™alubale da suka addabi yankin Arewa maso yamma a gaba ta hanyar kafa Hukumar BunÆ™asa Arewa maso yamma, domin kawo É—auki wajen magance matsalolin da suka addabi yankin tare da yin duk abinda yankin yake da buÆ™ata''. 

Wannan Æ™uduri zamu iya cewa shine abun alkairi mafi girma da Arewa maso yamma ta samu tun farkon wannan Majalisa ta 10, kuma zai shawo kan kaso mafi yawa na matsalolin da suka addabi yankin musamman a fannin ilimi, kiwon lafiya, tsaro, kasuwanci, noma da kuma tattalin arziÆ™i. 

Wannan Æ™udurin zai taimaka wajen dawo da masana'antun da ke ficewa daga jihohin yankin, su dawo su cigaba da gudanarwa a yankin, zai kuma kara yawaita ayyukan yi ga matasan jihohin wanda a yanzu kaso mai yawa na su ke zaune babu wadatattun ayyukan da zasu yi. 

Bisa dukkan alamu kuma kwalliya ta biya kuÉ—in sabulu, domin Æ™udurin ya samu goyon baya daga yan majalisar dattijai har 20 daga yankin Arewa maso yammacin kasar nan da ma ragowar yankunan, kuma tuni anyi karatu na 2 a gaban Majalisar. Hatta shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya goyi bayan kudirin inda ya bayyana cewa yankin na da tarin jama'a kuma buÆ™atar a bunÆ™asa yankin, abu ne da dace. 

Kamar yadda yankin Neja-Delta suke da hukumar bunÆ™asa yankin Neja-Delta, yankin Arewa maso Gabas ke da Hukumar bunÆ™asa Arewa maso gabashin Najeriya, wanda duka aka samar da su saboda wasu matsaloli da suka kawo cikas ga cigaban su, kuma samar da hukumomin ya haifar da abinda bahaushe ke kira 'É—a mai ido', to tabbas samar da Hukumar a arewa maso yamma zai zama cigaba mai É—orewa da za a mora a yankin da ma Najeriya baki daya. 

Allah ya taimaki Sanata Barau Jibrin Maliya, Allah ya taimaki Yankin Arewa maso yammacin Najeriya, Allah ya taimaki Najeriya. Ameen

-Aliyu Samba
Mataimaki na musamman ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya a kafafen sada zumunta. 
2/6/2024

No comments