Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Majalisun Tarayya Su Hada Kai Da Gwamnatin Neja Wajen Ganin An Dawo Da Aikin Madatsar Ruwan Baro

Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga yan majalisun tarayya masu wakiltar jihar Neja da su hada kai da Manomi gwamna Umar Bago wajen ganin...




Daga Awwal Umar Kontagora

An yi kira ga yan majalisun tarayya masu wakiltar jihar Neja da su hada kai da Manomi gwamna Umar Bago wajen ganin gwamnatin tarayya ta dawo da aikin madatsar ruwan Baro. Malam Zakari Mohammed Kuchi ( Zakarin Bima) ne yayi kiran a wata takardar manema labarai da ya fitar yammacin jiya littinin.

Matashin yace gwamnatin da ta gabata ta yaudari yan Nijeriya bisa cewar ta kammala aikin da ko damba ba a sanya masa ba, domin kammala aikin madatsar ruwan Baro zai taimaka wajen dawo da martabar noma a arewacin kasar nan, kasuwanci da samun karin ayyuka ga al'umma da samun hanyoyin kudaden shiga ga gwamnatin jiha da ta tarayya 

Yace tsohon shugaban kasa ya shelantawa duniya cewar an kusa kammala aikin madatsar ruwan, wanda maganar gaskiya duk wanda ya ziyarci wurin zai tabbatar batun ba haka yake ba, dan haka muna kira ga gwamnatin tarayya bisa jagorancin dattijo mai hangen nesa da ya dawo da aikin wannan madatsar zai kara masa kwarin guiwa tare da barin wani gibin alheri da ba za a manta da shi a arewacin kasar nan ba.

Da ya juya kan mukaman siyasa da gwamnatin Neja ta baiwa matasa, yace wannan abin a yaba ne, kuma ya nuna cewar matasan Neja ba su yi zaben tumun dare ba. Ina jawo hankalin duk wadanda suka samu mukaman siyasa da su yi koyi da halayen hadimin gwamna wajen kyautatawa jama'ar da suke tare da su, ba wai an ba su wannan damar kawai dan kan su da iyalan su ba ne. Domin da gwamna na son kan sa da bai raba irin wadannan mukaman ba, muna da kididdigar an bada mukaman siyasa a jihar Neja tsakanin gwamnatin jiha da jam'iyyar APC sama da dubu goma sha biyar, ya kamata sauran al'umma da ba su samu irin wannan damar ba, da su rika shaida cewar gwamnatin jiha tana tare da jama'a domin ku da ku ka samu mukaman wakilan gwamnati ne a wajen talakawa.

Kan maganar ayyukan raya kasa kuwa, yace matsayin da gwamnatin jiha take a yau matsayi ne na canja salon siyasar rashin kishin kasa da yunkurin azurta kai da tsoffin yan siyasa suka dogara akai, mu kan yanzu ba abinda za mu yi fata ga gwamnatin nan ta Umar Bago, sai fatar alheri da samun kwarin guiwar cigaba da wannan aikin alherin da ya somo.

Zakari Kuchi, ya nemi tsoffin yan siyasar da suke rike da mukaman siyasa kuma suka yi takara a baya suka sha kaye, da su sani wannan izina ce gare su, domin ba wai yawan ayyuka a kasa ba kyautatawa jama'a ba ne iya siyasa da ruwan ciki fa ake jan na rijiya tsari da salon siyasar Rt. Hon. Umar Bago ya isa misali ga masu sha'awar tsayawa takarkarun siyasa a gaba.

Matashin yace shekara dayan Umar Bago kan karagar mulki yafi shekaru takwas na shugabancin wasu, domin nan da shekaru hamsin sunan Umar Bago ba zai shafe a doron kasa ba, sakamakon kudurin alheri da son cigaban jiha da al'ummar jihar Neja da ke zuciyarsa.

Kuchi, ya nemi yan majalisun tarayya da na jiha, da su ajiye maganar jam'iyya su fuskanci nauyin da ke kan su, saboda da zaran an kammala zabe maganar jam'iyya ya kare al'umma da kasa ne a gaba.

No comments