Daga Idris Umar, Zariya Dakta Hasan Gimba mawallafi jaridar yanar gizo mai suna NEPTUNE PRIME dake babban birnin tarayya Abuja. A mahangar...
Daga Idris Umar, Zariya
Dakta Hasan Gimba mawallafi jaridar yanar gizo mai
suna NEPTUNE PRIME dake babban birnin tarayya Abuja. A mahangar hankali kafin
ka yabi mutum ka je kusa da shi ko ka zauna kusa da shi za ka gane ko wane ne
shi.
Haka zalika idan kana so ka gane mutum ko shi wane ne
ka barshi ya yi magana tukunna daga nan zaka gane wane ne shi. Ba kasafai na
kan ware lokaci na yi rubutu akan wani ba amma ance yabon gwani ya zama dole
kuma ko da naka kakan so na kwarai.
Dakta Hasan Gimba mawallafin jaridar NEPTUNE PRIME mutum
ne mai kishi harkar yaÉ—a labarai, mai son ci gaban gidajen jaridu gida da waje
matukar ya hangi adalci a cikin tafiyar.
Bari na yi amfani da wannan lokaci wato lokacin da
mawallafi ke gudanar da ziyara tare da yin addu'a a muhallin da iyayensa ke kwance wato makabartar NEPA dake
garin Potiskum ta jihar Yobe.
Cikin alhini muna roko tare da fatan Allah ya ƙarbi
ziyarar tashi da dukkan addu’o’in da ya yi wa iyaye nasa a lokaci baya da kuma
daidai wannan lokacin.
Wato yin amfani da wannan lokacin ne zai sa jama’ar
da muke tare da su na nesa da na kusa su fahimci abin da nake nufi ga hazikin
mawallafin kuma abokin tafiya ga duk wani dan jarida a kasarmu da duniya baki
daya.
Dakta Hassan Gimba ya zama na gaba-gaba a wajen janyo
hankalin gwamnati tarayya da gwamnatin jihohi da ƙananan hukumomi a duk lokacin
da ya hango suna ƙoƙarin tafka kuskure a kowanne ɓangare musamman wuraren da
suka zama Æ™ashin bayan mulkin jama’a kamar harkar lafiya da harkar Ilmi da abin
da ya shafi tsaro da dai sauransu.
Dakta Hasan yana daga cikin mutanen da ake girmamawa
a arewa da kudu a ɓangaren hasashen da bayar da shawara a jaridance kuma a
hukumance. Kuma an shaidi kafar yaɗa labaransa wato Neptune Prime da ƙokarin
kare mutuncin al’ummar Æ™asa baki daya.
Dakta Hassan Gimba mutum ne da ko wani yaro zai so
ya zama ubansa kuma ko wani dattijo zai so ya zamo ɗansa a ɓangaren
zamantakewar juna. Mun shaide shi da kare mutuncin kansa wajen kaucewa yin
karya a cikin harkokinsa babu cin amana kuma.
Gimba mutum ne mai dauriyar a lokacin da ba yi da shi
kuma samun sa baya sashi girman kai ga
naÆ™asa da shi. Bisa haka ne muke wa kasarmu addu’a Allah ya yawaita irinsu
Dakta Hassan Gimba domin aikin alheri su Æ™aru a ko’ina a faÉ—in Æ™asa.
Farko bayan gaisuwa na girmamawa zanyi ta’aziyya na rashin
da aka yi masa na rasuwar Alhaji Gimba Ahmad (Baba) wanda mahaifi ne gare shi da
Hajiya Hafsatu Gimba Ahmad (Mama) wacce mahaifiya ce gare shi, sai matarsa
Hajiya Fatimah Balarabe, Allah ya gafarta masu baki É—aya.
Wani abin ban sha’awa ga mawallafin jaridar ta
Neptune Prime dake Abuja wato Dakta Hasan Gimba, mutum ne haziki mai hangen
nesa shiyasa ma da yawan ma’aikatansa ke masa lakabi da Babanmu.
Alhaji Hasan Gimba mutum ne mai tausayin al’umma
yana jan kowa a jika don sanin me ke damun sa don bayar da taimako a gare shi.
Dan binciken da muka yi ya nuna Gimba yana bacci ne
ƙalilan domin da yawan harkokinsa nazarce nazarce ne kawai kuma wani abin ban
sha’awa shi ne yana bayar da hankalinsa ne a É“angaren wayar da kan al’umma ba don
neman abin duniya ba amma in ya samu ya kan nuna godiya ga Allah don zai yi
kyauta har da sadaka ga jama'ar da yake tare da su.
Dakta Hassan
Gimba ya gaji mahaifinsa ne Alhaji Gimba Ahmad wajen yima al’umma hidima. Mahaifin
Dakta Hasan Gimba wato Alhaji Gimba Ahmed shima ya yi fice a wajen taimakon al’umma
da Æ™wantar da hankalin jama’ar dake zaune kusa da shi.
Shiyasa ma a lokacin rasuwar mahaifin nasa duk wani
babban mutum dake jihar Yobe sai da ya
girgiza da rasuwar Alhaji Gimba Ahmad. Al’ummar jihar Yobe sun yi kukan rashin
Alhaji Gimba Ahmad a cikinsu. Amma abin da Allah ya tsara babu yadda za a yi
sai ya faru Allah ya sanyaya maƙwancin Alhaji Gimba Ahmad yasa Aljanna
makomarsa.
Maganar da manya kan faÉ—a cewa duk idan kagga
Gwarzon namiji to akwai jarumai mace kusa da shi wannan lamarin haka yake domin
Dakta Hasan Gimba ya gado wasu kyawawan É—abi'un ne daga wajan mahaifiyarsa
musamman halin nan nasa na son taimakawa na ƙasa da shi wanda suka san
mahaifiyar Dakta Hassan Gimba wato Hajiya Hafsatu Gimba Ahmad, sun yi mata
kyakkyawar shaida wajen son mutane kuma an tabbatar abin hannunta bai taba rufe
mata idanu ba. Tana da tausayi sosai ta kuma taimakawa maigidanta Alhaji Gimba
Ahmad a ɓangaren kyautata alaƙarsa da mutanen garin Potiskum da jihar Yobe baki
daya. Allah ya kai haske ga kabarinsu baki daya.
Hajiya Lami Fatima Balarabe ita ce matar Dakta Hasan
Gimba wanda Allah ya yi mata rasuwa babu daÉ—ewa. Hajiya Lami Fatima kallabi
tsakanin rawuna, mace kamar maza kafin komawa ta ga Allah ta bar tarihi masu
yawa a ɓangaren kula da maigidanta da danginsa da abokan zamanta da abokan
arziki da suke tare da shi. Allah ya jiƙanki da rahamarsa.
Hajiya Lami ta koma ga Allah a hannun maigidanta
Dakta Hasan Gimba wanda mutane dubbai ne
suka yi masa jaje a yayin da ya sanar da rasuwar ta a shafinsa na sada zumunta
wanda hakan ke nuna cewa Hajiya Lami ta koma ga Allah yayin da ake kaunar ta
wanda hakan alama ce ta samun rahama.
Hajiya Lami Fatima har yanzu al’umma na jin daÉ—in
ababen alherin da kika kafa a zuciyar mijinki. Bisa haka ne muke rokon Allah ya
kai rahama gareki da sauran iyayen mu da suka rigamu gidan gaskiya.
Idris Umar ya rubuta, za a iya samunsa a adireshin
imel kamar haka: idrisu081@gmail.com
No comments