Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dawo Da Muhammadu Sanusi Kujerar Sarautar Kano, Gwamnatin Abba Ta Kyautawa Kanawa - Bichi

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar dawo da Muhammadu Sanusi kan kujerar sarautar Kano an kyautatawa kanawa kuma an dawo da martabar ...

Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar dawo da Muhammadu Sanusi kan kujerar sarautar Kano an kyautatawa kanawa kuma an dawo da martabar sarautar gargajiya mai din bin tarihi. Wani matashin dan kasuwa dan asalin Bebejin jihar Kano, Alhaji Shu'aibu Aliyu Bichi ne ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai a Minna.

Bichi, ya cigaba da cewar farfasa marasautar Kano tamkar wulakanta sarautar Kano ce da ta gaji hadin kai, zaman lafiya da soyayya ga kanawa. Wannan abinda gwamna Abba Yusuf Kabir yayi na dawo da Muhammadu Sanusi II mun gamsu da cewar gwamnatin Abba tayi abinda ya dace.

Masarautar Kano tana bukatar gogagge kuma fasihi wanda ya damu da damuwar al'ummarsa, wanda duk abinda zamani ke bukata a tafiyar da jagoranci mai martaba Muhammadu Sanusi II yana mallake su.

Ina kira ga kanawa duk wani mai son cigaban Kano, kuma ya amince da cigaba na gaskiya yake muradi, ya baiwa mai martaba goyon baya, sannan ya yiwa gwamnatin Abba Yusuf Kabir fatan alheri sannan ya rungumi zaman lafiya.

Da ya juya kan cikar Abba Yusuf Kabir shekara daya a karagar mulkin gwamnatin Kano, kuwa yace ayyukan da Abba ya sanya a gaba yanzu kanawa sun dade suna mararinsa, idan ka dubi bangaren ilimi da kiwon lafiya an dauko hanyar dawo da martabarsu. Domin tallafin karatu da gwamnatin Abba ta baiwa al'ummar Kano wani ginshiki ne da zai anfanar a gaba.

Yace maganar farfado da kanfanonin da suka durkushe a jihar Kano, matsalar gwamnatin tarayya ce, domin koda gwamnati ta umurci babban bankin Nijeriya ta baiwa yan kasuwa rancen kudade, abin ba zai yi tasiri ba dole sai an rugurguje darajar dala.

Kanfanoni na biyan haraji na fitar hankali, ruwan da bankuna ke sanyawa wadanda aka baiwa rance ba zai ba su kwarin guiwar da zasu iya zama da kafarsu ba, dole gwamnati ta saukaka haraji, bankuna su rage yawan kudin ruwa idan har da gaske ana bukatar kanfanonin kasar nan su dawo cikin hayacin su.

Matashin ya shawarci matasa da su koma gona domin noma itace rayuwa, duk irin matsin da za a shiga muddin ba abinci lallai ba wani matakin da za a dauka da zai sa a samu nasara.

Matashin ya roki al'ummar Kano da su kauda bambance bambancen da ke tsakanin su na siyasa ko biyayya ga wani, da su dawo su sanya jihar Kano gaba akan komai. Kar su yarda radadin gyaran targade yasa makiya su yi masu dariya, domin wasu shugabanni marasa kishin Kano sun dade suna neman hanyar da jihar Kano baya, sun dade suna neman rugurguza tarihin zaman lafiya da kasuwancin da aka san jihar Kano a kai.

No comments