Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE
Friday, June 6

Pages

Labarai:

A Shirye Nake Na Koma Saudi Arabia Da Taka Leda - De Bruyne

ÆŠan wasan Manchester City, Kevin de Bruyne ya ce "A shirye nake na rungumi dukkan damar da za tatunkare ni'' bayan da yake tatt...


ÆŠan wasan Manchester City, Kevin de Bruyne ya ce "A shirye nake na rungumi dukkan damar da za tatunkare ni'' bayan da yake tattauna kan komawa Saudi Arabia.

Ɗan kasar Belgium, mai shekara 32, yana da sauran kaka daya da City, ƙungiyar da ya lashe Premier League shida da Champions League tun bayan da ya koma Etihad a 2015.

De Bruyne ya ce " Zan yi murna da zarar na samu ƙwantiragi mai tsoka don buga babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia - lokacin da yake shirin kammala sana'ar tamaula.

Ya kuma kara da cewar ya tattauna da matarsa kan lamarin, domin samun mafita tun kafin lokacin ya yi.

''Ina da sauran yarjejeniyar kaka daya a Etihad, saboda haka ina da lokacin tunanin abinda ya kamata na yi tun kan lokaci ya kure.

''Babban É—ana yanzu yana da shekara takwas, kuma bai san komai ba sai Ingila. Ya kuma tambaye ni ko yaushe zan kammala wasa a City, amma da zarar lokaci ya yi zan samu mafita.

''A shekarun da nake da su a yanzu ya kamata na rungumi duk wata damar da za ta zo min. Za ka iya tunanin yadda za ka karkare rayuwar sana'ar tamaula. Kuma koda yaushe abinda ke ranka kenan.''

De Bruyne ya kara da cewar da zarar ya yi kaka biyu a Saudi Arabia yana taka leda, zai samu makudan kudin da yake bukata.''

Ƙyaftin ɗin tawagar Belgium, wanda zai buga Euro 2024, ya sha jinyar wata biyar a bara, inda City ta dauki kofi hudu, wanda ya buga karawa 26 a dukkan fafatawa.

No comments