Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Watakila Odegaard Ba Zai Buga Wasan Tottenham Da City Da Atalanta Ba

  Watakila Martin Odegaard ba zai buga wa Arsenal gasar Premier League da za ta yi da Tottenham da Manchester City da na Champions League Le...

 


Watakila Martin Odegaard ba zai buga wa Arsenal gasar Premier League da za ta yi da Tottenham da Manchester City da na Champions League League ba.

Hakan ya biyo bayan raunin da ya ji a kafa a Nations League da Norway ta kara da Austria ranar Litinin.

Ƙyaftin ɗin tawagar Gunners ya ji rauni ne sakamakon ketar da Christoph Baumgartner ya yi masa a karawar da Norway ta ci 2-1 a birnin Oslo.

Masana sun ce irin raunin da Odegaard ya ji kan sa É—an wasa ya yi jinyar mako uku kafin ya warke, watakila ya warke kafin nan ko kuma ya haura.

Arsenal za ta je gidan Tottenham a wasan mako na huÉ—u a Premier League ranar Lahadi 14 ga watan Satumba.

Daga nan Gunners za ta je Italiya, domin fafatawa da Atalanta a wasan farko a cikin rukuni a Champions League ranar Alhamis 19 ga watan Satumba.

Haka kuma Gunners za ta je Etihad domin fuskantar Manchester City a wasan mako na biyar a Premier League ranar 22 ga watan Satumba.

Norway za ta buga wasan gaba a Nations League da Slovenia ranar 10 ga watan Oktoba a Oslo, kwana uku tsakani ta fafata da Austria a Linz.

No comments