Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mutum 37 Ne Suka Mutu A Ambaliyar Maiduguri - NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta ce kimanin mutum 37 ne suka mutu sakamakon mummunar ambaliya ruwa da ta auka wa birnin ...


Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta ce kimanin mutum 37 ne suka mutu sakamakon mummunar ambaliya ruwa da ta auka wa birnin Maiduguri.

Yayin zantawarta da BBC shugabar hukumar Hajiya Zubaida Umar ta ce akwai fargabar Æ™aruwar waÉ—anda iftila'i ya shafa, yayin da ma’aikatan hukumar ke cigaba da aikin ceto waÉ—anda suka maÆ™ale.

Hajiya Zubaida ta kuma ce fiye da mutum 400,000 suka rasa muhallansu sakamakon bala'in.

Ambaliyar ruwa dai ta auku ne sakamakon ɓallewar madatsar ruwa da Alau da ke wajen birnin.

Shugabar hukumar NEMAn ta kuma bayyana ambaliyar a matsayin mai tayar da hankali.

''Abin akwai tashin hankali, don ruwa ya cinye garin Maiduguri ba kaÉ—an ba, ga mutane nan kana gani an koro su daga gidajensu'', in ji ta.

Ta ce ambaliyar ta cinye kusan kashi 40 cikin 100 na birnin Maiduguri.

Hajiya Zubaida ta ce har kawo yanzu akwai mutanen da ba a iya ceto su ba bayan da suka maƙale cikin ɓaraguzan gine-gine.

Ta ƙara da cewa jami'an hukumar na ci gaba da aikin ceto mutanen da ambaliyar ta rutsa da su.

''Yanzu haka da nake magana jami'an hukumarmu a cikin unguwanni domin ci gaba da zaƙulo mutanen da har yanzu ke maƙale cikin gidajen da ruwa ya cinye'', in ji shugabar hukumar ta NEMA

Tuni da gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya ce fiye da mutum miliyan guda ne ambaliyar ta shafa.


'Mun tanadi asibitocin tafi-da-gidanka'

Hukumar NEMA ta ce tuni aka buÉ—e sansanonin 'yan gudun hijira takwas a faÉ—in birnin domin tsugunar da waÉ—anda suka rasa muhallansu.

Haka kuma an tanadi abinci da kwale-kwale da ƙananan jiragen ruwa domin taimaka wa aikin ceton.

Haka kuma shugabar ta NEMA ta ce hukumar ta tanadi motocin tace ruwan sha domin daƙile ɓarkewar cutuka sakamakon ambaliyar.

Hajiya Zubaida ta kuma ce hukumarta ta tanadi tantunan masu yawa domin taimaka wa mutanen da ba su samu matsugunai a sansanonin 'yan gudun hijirar ba, da su kafa domin samun mafaka.

Ta kuma ƙara da cewa hukumar ta tanadi asibitocin tafi-da-gidanka da magunguna da kuma likitoci domin bayar da magani ga waɗanda ke buƙatar kulawar likitocin.

Ambaliyar ta cinye muhimman gine-gine

Hajiya Zubaida ta kuma ce ambaliyar ta haddasa mummunar ɓarna a birnin, inda ta cinye muhimman gine-gine ciki har da babban asibitin birnin, da gidan adana namun daji da kuma wani gida yari.

Shugabar Hukumar ta NEMA ta kuma yaba wa gwamnatin tarayyar ƙasar da ma'aikatar lafiyar da gwamnatin jihar Borno da Hukumar Lafiya da Duniya, WHO bia taimakon da ta ce sun bayar wajen daƙile ambaliyar.

A nasa ɓangare gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya tabbatar da karɓar tallafin naira biliyan uku daga gwamnatin tarayya, wanda ya ce za a yi amfani da shi wajen agaza wa waɗanda lamarin ya shafa.

Ya ce gwamnati za ta kafa wani kwamitin lafiya domin duba daƙile yiwuwar ɓarkewar cutuka a sansanon 'yan gudun hijirar.


No comments