Daga Idris Umar Zariya A cikin wannan satin ne Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Maƙarfi da Kudan a Jihar Kaduna Honorabul Umar Shehu Ajino...
Daga Idris Umar Zariya
A cikin wannan satin ne Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Maƙarfi da Kudan a Jihar Kaduna Honorabul Umar Shehu Ajino ya ƙaddamar da horon kiwo Kifi da sauran Dabbobi ga matasa 200 a yankin da yake wakilta.
Wakilinmu ya sami halartar taron. Taron an gudanar da shi ne a babban É—akin taro na makarantar horar da sana'o'i na Isa Ashiru dake garin Kudan.
AGARD FARM LMTD sune suka jagoranci bayar da horon karkashin shugabantar mista Husaini Isa (maji Dadi).
An sami malaman gona a ɓangarori daban daban da suka gabatar da muƙaloli dake koyar da kiwon a zamanance cikin sauke
Dakta Yusuf Adam, na cikin wanda suka bayar da horon ya shaidawa manema labarai cewa, sun gabatar da horo ga mutane 200 maza da mata kuma horon ya sami karɓuwa sosai, sun koyar da yadda ake kiwon kifi cikin sauki tare da nuna wa mahalarta taron nasarar da ake samu a kiwon kifin da kuma yadda ake magance ƙalubalen dake cikinsa.
Ƙarshe ya yabawa Honorabul Ajino bisa wannan kokari kuma yayi fatan mahalarta taron za su yi amfani da karatun da suka samu.
Shima Farfesa Lawal Sa'eed, Maƙarfi wanda yana daga cikin wakilan Honorabul Ajino a wannan ƙoƙari cewa ya yi horon an assasa shi ne don matasa su sami abin rike kansu don rage raɗadin talauci da kawo ci gaban arziki a karamar hukumar Kudan da ƙasa baki ɗaya.
Ƙarshe ya yi fatan Alheri ga shi wanda ya dauki nauyin horon Honorabul Ajino da cibiyar da take bayar da horon wato AGARD FARM LMTD da shugan dake jagorantar ta.
Shima Honorabul Halliru M .Sule (excellence) yana daga cikin masu sanya Idanu a wannan horo da ake bai wa matasa 200 a Maƙarfi da Kudan kuma yana daga cikin na hannun damar dan majalisan na su.
Shima a nasa jawabin ga manema labarai a yayin kammala taron ya tabbatar wa al'ummar ƙaramar hukumar Kudan basuyi zaben Tumun dareba a jamɓiyar PDP.
Ya ce,wannan kokarin na daga cikin burin da É—an majalisar tarayyar su yake dashi a cikin zuciyarsa.
Bisa haka ne, Honorabul Halliru ya yi kira ga al'ummar karamar hukumar Kudan da su bai wa Honorabul Ajino haÉ—in kai don ci gaban wannan karamar hukumar ta su.
Malama Rashidat, daga garin Gubuci na cikin wanda suka sami horon kuma ta tabbatar za suyi kiwon Kifi kamar yadda aka koya masu karshe tayi fatan Alheri ga shi wanda ya dauki nauyin bayar da horon.
An yi taro lafiya an tashi lafiya.
No comments