An dakatar da ɗan wasan Chelsea Enzo Fernandez daga tuƙi na tsawon watanni shida, sakamakon aikata laifukan a tuki har sau biyu a yammacin...
An dakatar da ɗan wasan Chelsea Enzo Fernandez daga tuƙi na tsawon watanni shida, sakamakon aikata laifukan a tuki har sau biyu a yammacin Wales.
Tuni dai aka samu ɗan wasan ƙwallon ƙafar tawagar Argentina da laifin kasa tantance direban wata mota ƙirar Porsche da ake zargin ya tuka wanda ta keta dokokin tuƙi a ungwar Llanelli da ke yankin Carmarthenshire a watan Nuwamban 2023.
An kuma sami matashin mai shekaru 23 da irin wannan laifin da ya shafi wannan motar ƙirar Porsche da ake zargin an kama ta da laifin gudun da ya wuce misali a Swansea wata guda bayan haka..
Fernandez, wanda aka ci tararsa fam 3,020, bai bayyana a kotun Majistare ta Llanelli a ranar Laraba ba, bayan da ya buga wa Argentina wasa a Colombia ranar Talata.
Ba a tabbatar da cewa Fernandez ne direban motar ba a lokutan biyu, amma an bayyanawa kotun cewa bai amsa buƙatar ƴan sandan yankin Dyfed-Powys da na yankin South Wales na neman bayanai game da direban motar ba.
No comments