Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Uba Sani Ya Yi Wa Fursunoni 110 Afuwa Saboda Ranar Dimokuradiyya

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi wa fursunoni 110 afuwa a wata ziyara da ya kai a babban gidan gyara hali da ke cikin garin Kaduna. Gwam...



Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi wa fursunoni 110 afuwa a wata ziyara da ya kai a babban gidan gyara hali da ke cikin garin Kaduna.

Gwamnan ya ɗauki matakin ne a ranar Talata, kwana ɗaya gabanin bukin ranar dimokuraɗiyyar ƙasar wanda zai gudana a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu.

Uba Sani wanda ya kuma bai wa fursunonin da aka yi wa afuwar naira 30,000 a matsayin kuÉ—in mota.

No comments